Hukumomi a Saudiyya sun sanar da kame maniyyata dubu 300 wadanda ba su da takardun shaidar aikin hajjin bana
ASSALAM ALAIKUM YAU LITININ 04 GA ZUL HAJJI 1445 10 GA YUNI 2024 🇳🇬Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, NDLEA ta ce jami'an ta sun kama kwalba 175,000 ta miyagun ƙwayoyi da maganin tari da aka shigar da su ƙasar daga India. Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce sun yi wannan nasarar ne mako guda bayan wata irin ta da suka samu, inda suka kama hodar ibilis da aka shiga da ita Najeriyar, a jihar Rivers. Ya yi bayanin cewa NDLEA da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro ta yi nasarar kama kayan laifin ne a ranar juma'a, 7 ga watan Yunin bana, bayan sun nemi gudanar da cikakken bincike a kan kayan da aka shigo dasu daga ƙasashen waje. 🇳🇬Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince a biya albashin watan Yuni ga ma'aikatan jihar daga ranar Litinin. Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne domin bai wa ma'aikatan gwamnatin jihar damar yin bikin babbar sallah cikin walwala. Sakataren yaɗa labaran gwamnan Sokoto, Abubakar Bawa, ya ce dukkan ma'aikatan jihar,