Hukumomi a Saudiyya sun sanar da kame maniyyata dubu 300 wadanda ba su da takardun shaidar aikin hajjin bana

ASSALAM ALAIKUM 

YAU LITININ

04 GA ZUL HAJJI 1445

10 GA YUNI 2024


🇳🇬Hukumar hana sha da
 fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, NDLEA ta ce jami'an ta sun kama kwalba 175,000 ta miyagun ƙwayoyi da maganin tari da aka shigar da su ƙasar daga India.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce sun yi wannan nasarar ne mako guda bayan wata irin ta da suka samu, inda suka kama hodar ibilis da aka shiga da ita Najeriyar, a jihar Rivers.

Ya yi bayanin cewa NDLEA da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro ta yi nasarar kama kayan laifin ne a ranar juma'a, 7 ga watan Yunin bana, bayan sun nemi gudanar da cikakken bincike a kan kayan da aka shigo dasu daga ƙasashen waje.


🇳🇬Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince a biya albashin watan Yuni ga ma'aikatan jihar daga ranar Litinin.

Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne domin bai wa ma'aikatan gwamnatin jihar damar yin bikin babbar sallah cikin walwala.

Sakataren yaɗa labaran gwamnan Sokoto, Abubakar Bawa, ya ce dukkan ma'aikatan jihar, da na ƙananan hukumomi da kuma ƴan fansho ne za su amfana da wannan karamci.

Abubakar Bawa, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da biyan albashin ma'aikata a kan lokaci, kamar yadda ya ce ya zama al'adar gwamantin, biyan albashi a ranar 20 zuwa 21 na kowanne wata, tun bayan karɓar ragamar mulki.



🇳🇬 Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda zai baiwa ma’aikatan jiha da kuma na kananan hukumomin Katsina naira 45,000 domin gudanar da bukukuwan Sallah.

Sai dai Gwamnan ya ce N15,000  cikin kudaden kyauta ne amma sauran N30,000 rance ne da za a cire daga albashinsu nan da watanni uku masu zuwa.

🇳🇬Hukumar Alhazai ta jihar Kwara na mika sakon ta’aziyya ga iyalan mahajjatannta biyu da suka rasu a birnin Madina na kasar Saudiyya.

Saliu Mohammed, wanda ya zo a rukunin Batch 3 na tawagar jihar, ya rasu ne a sashin kula da marasa lafiya na wani asibitin gwamnati da ke Madina bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Ita kuwa Hajiya Hawawu Mohammed ta rasu ne biyo bayan wani bincike da hukumomin Saudiyya suka yi, inda suka gano cewa ta faɗo ne daga saman benen Otel ɗin da ta ke a Madina.

🇳🇬Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Kaura-Namoda/Birnin-Magaji, Aminu Jaji, ya sayi raguna 3000 don raba wa jama’ar mazaɓarsa da kuma ‘ya’yan jami’yyar APC a Jihar Zamfara.

Ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin gudanarwar Jaji, Aliyu Abubakar, ya sanya wa hannu a ranar Asabar.

A cewar sanarwar, Jaji ya kuma ware Naira miliyan 250 don raba wa mutane, marayu, da ƙungiyoyin agaji a faɗin jihar, don gudanar da bikin sallah cikin walwala.

“Wannan wata dama ce da ke zuwa shekara-shekara da nufin taimaka wa musulmi, musamman ’yan jam’iyyar APC da marasa ƙarfi, don yin bikin sallah cikin walwala

DAGA ƘASASHEN WAJE 
🌍Hukumomi a Saudiyya sun sanar da kame maniyyata dubu 300 wadanda ba su da takardun shaidar aikin hajjin bana da ake shirin farawa a makon gobe.

A cewar Saudiya, matakin bibiyar wadanda ba su da shaidar aikin hajjin na da nufin rage cunkoson jama’a, a yayin ibadar wadda kan tattara miliyoyin mutane daga sassa daban-daban na duniya.
Sanarwar da hukumar kula da cunkoson jama’a ta Saudiyya ta fitar ta ce cikin wadanda mutane har da dubu 153 da 998 da suka shiga kasar da takardar yawon bude ido sabanin takardar izinin aikin hajji da ya kamata su samu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya ce daga cikin mutanen akwai kuma wasu dubu 171 da 587 wadanda suke zaune a kasar ta Saudiyya amma ba ‘yan asalin kasar ba, kuma suka fito da nufin aikin hajjin ba tare da takardun izini ba.
🌍Ranar Litinin din nan ce ranar da hukumomin ƙasar Saudiyya suka tsayar mastayin ranar cikar waadin kammala jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga kowace kusurwa ta duniya.

Da karfe 12 na tsakar daren yau Litinin agogon Saudiyya ne hukumomin na Saudiyya suka ce za su rufe filayen jiragen saman ƙasar 6 ga saukar duk wani jirgin da ya dauko maniyyata daga kowace kasa ta duniya.

Hakan ya sa ƙasashe musamman waɗan da ke da adadi mafi yawa na maniyyatan da ke rige-rigen ganin sun kammala jigilar maniyyatansu kafin cikar wa’adin.

Filayen jiragen su ne waɗan da aka keɓe domin jigilar maniyyatan na bana da ke biranen Riyadh, da Jiddah, da Madina, da Dammam, da Taif, da kuma Yanbu’u.


🌍Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta zargi takwararta ta Jamhuriyar Benin da yin garkuwa da jami'anta da ta kama a tashar fitar da man dake birnin Cotonou. Sanarwar da kakakin gwamnatin sojin Kanar Abderrahmane Amadou ya bayyana haka a sanarwar da ya karanta ta kafar talabijin. Kakakin gwamnati ya kuma zargi Benin da sabawa yarjeniyoyin da kasashen biyu suka rattaba hannu a kai wadanda suka shafi gina bututun mai daga Nijar zuwa Benin da kuma fitar da shi zuwa kasuwannin duniya. Yanzu haka wannan takaddama tsakanin kasashen biyu dake makotaka da juna na yiwa aikin fitar da man Nijar zuwa kasuwannin duniya barazana.


............,.........,.......

Allah ya gafarta mana zunuban mu ya haɗa mu da alherin wannan rana ta Litinin.
..................................
MARUBUCI MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE

Comments

Popular posts from this blog

Kotun kolin kasar nan ta sanya yau Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar

Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal