Kotun kolin kasar nan ta sanya yau Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar

Yau Juma'a 07--Rajab-1445
19-Janairu 2024
⚖️Kotun kolin kasar nan ta sanya yau Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar. Jihohin da kotun zata yanke hukunci kan kararrakinsu idan Allah ya kaimu yau sun haɗa da Ogun, Kebbi, Nasarawa, Gombe da kuma Delta.
🤓Shugaban jam’iyyar APC na riko Dakta Abdullahi Ganduje ya ce 'yan siyasar Nijeriya sune da alhakin tabarbarewar harkokin zabe a Nijeriya.
🥹Gwamna Dauda Lawal Dare ya rattaba hannu a kan dokar haramta wa sarakunan gargajiya ba da izinin hakar ma’adinai a fadin Jihar Zamfara.
  Dokar wadda ta fara aiki nan take an sanya mata hannu a wannan Alhamis din a Fadar Gwamnatin Zamfara da ke Gusau.
Cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnatin jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa dokar da gwamnan ya sanyawa hannu za ta dakile ababen da ke kara rura wutar ta’addancin ’yan bindiga a jihar.
    Mai magana da yawun gwamnan ya ce wannan doka ta dakatar da duk wata takardar ba da izinin hakar ma’adinai “wadda ta hada da daidaikun mutane ko kamfani ko kungiyoyi dake aiyukkan hakar ma’adinai.”
🧐Gwamnatin jihar Sokoto ta kwato motoci 70 cikin 745 da aka ce a gwamnatin da ta gabata wadanda tsoffin jami’an gwamnatin jihar suka daka wa,wawa.
Shugaban kwamitin kwato kadarorin gwamnati jihar ne, Alhaji Jelani Kalgo ya bayyana haka a lokacin da yake mika rahoton riko na kwamatin ga gwamna Ahmed Aliyu a ranar Alhamis.

 A cewarsa, motoci 745 ne kwamitin ya tantance.

 Ya ce, “Motoci 302 na hannun tsofaffin kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da manyan jami’an gwamnati yayin da 443 ke hannun jami an kananan hukumomi.

 “Ya zuwa yanzu mun kwato motoci 32.
Yace "Mun zaga dukkan kananan hukumomi 23, muka gano cewa kashi 70 cikin 100 na motoci 443 da ke kananan hukumomin Duk sun lalace"

 “Kuma kwamitin ya gano cewa an saka wasu motoci kusan 40 a matsayin motocin haya Inda wadanda suka saci motocin Ke amfana fa kudin hayar motocin. Sannan wasu motocin Kuma an fice da su daga jihar zuwa wasu jihohi Ko Kuma an tsallaka dasu zuwa kasashen makwabta.
🍲💊Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC)  ta kama katan 24 na maggi dunkule da lokacin amfaninsa ya kare da kudinsu ya kai kimanin Naira miliyan 4.5 a jihar Sokoto.

🧙‍♂️Wanī Babban lauya a Najeriya, Inibehe Effiong ya soki gwamnonin da suka yi nasara a Kotun Koli. Lauyan wanda ke zaune a Legas ya ce abin kunya ne yadda gwamnonin ke yabawa Shugaba Tinubu bayan sun samu nasara. 
Idan ba a mantaba, Gwamna Abba Kabir na Kano ya yabawa Tinubu kan irin kokarin tsame hannunsa a lamarin shari'ar. 
Har ila yau, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da takwaransa na Plateau duk sun yabawa shugaban. A ranar 12 ga watan Janairu ce aka yanke hukuncin zaben jihohi 8 da suka da da Kano da Bauchi da Plateau da Zamfara.
Effiong ya ce abin mamaki ne yadda suka yi ta godewa Tinubu kamar alkalan Kotun Kolin don Tinubu suke yin hukunci.
🧐Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hoki da ke Jihar Kano ta gurfanar da dan siyasar nan Garzali Musa Obasanjo bisa zargin bata sunan Malam Lawan Triumph, daya daga cikin fitattun malaman sunnah a jihar.
Majiyar mu ta ruwaito cewa, wani shakikin malamin mai suna Muhammad Sani Abubakar ne ya kai wa ’yan sanda karar Obasanjon kan zargin batanci da taba muhibbar mahaifiyar Malam Lawan Triumph din da ’yan uwansa a shafin sada zumunta na Facebook.
A zaman kotun na ranar Alhamis, bangaren masu kara sun nemi a ba su ranar da za su gabatar da shaidu kan wannan tuhuma ta batanci da ake yi wa Obasanjon.
Kan haka ne Alkalin Kotun, Malam Abdullahi Halliru ya amince da bukatar, ya kuma dage zaman ci gaba da sauraron shari’ar zuwa  ranar 13 ga watan Fabrairu 2024.


DAGA KASASHEN WAJE
🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍

💊Hukumomin kasar Mozambique sun damu da wata bakuwar cuta da ta kashe sama da shanu 900 a yankin tsakiyar kasar tun watan Disamba.
  Masu kiwon dabbobi da hukumomin kula da dabbobi ba su san cutar ba.
  Ya barke ne a lardin Manica da ke kan iyaka da Zimbabwe kuma ya bazu zuwa gundumomi uku na lardin.
Masu kiwon dabbobin da suka damu suna neman daukin gaggawa daga hukumomin kula da dabbobi domin hana asara, a daidai lokacin da ake fargabar cutar na iya yaduwa tare da kashe wasu shanu.



 💉Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ce an kashe mutum 93 da suka haɗa da mutum 16 ƴan gida ɗaya a harin a birnin Rafah da ke kudancin Gazan, wajen da mutane da yawa suka tsere daga cikinsa...

DAGA FAGEN WASANNI
⚽⚽⚽⚽⚽🏐🏐🏐
Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta samu nasarar doke kasar Ivory Coast a Gasar Kofin Afirka ta AFCON 2023 da suka fafata a Yammacin ranar Alhamis a Abidjan.

Super Eagles wadda ta samu nasarar farko a gasar wadda aka soma a wannan makon, ta yi wa Ivory Coast wadda ita ce mai masaukin bakin ci daya mai ban Hashmi yayin aragamar da aka yi a filin wasa na Alassane Outtara da ke birnin Abidjan.
Kwallo daya ce ta raba gardamar da aka kwashe minti 90 ana yi, inda kyaftin din Super Eagles, William Troost-Ekong ya kankaro wa ’yan Najeriya martaba a bugun daga kai sai mai tsaron raga da ya jefa a minti na 54.

Wannan shan kashi da tawagar ta Ivory Coast ta yi ita ce rashin nasara ta farko aka samu wata kasa mai masaukin baki ta yi a wasannin rukuni tun bayan wadda Equatorial Guinea ta yi a shekarar 2012 lokacin da ta yi hadakar saukar baki.




🏐 A dayan wasan Kuma a rukunin B, an tashi wasa tsakanin Egypt 2-2 Ghana a gasar cin kofin nahiyar Afrika AFCON.Sai dai dukkanin wadannan kasashen zasu San makomar su ne a wasa na gaba Ko a ci gaba da su Ko Kuma anyi waje road da su



⚽Atletico Madrid ta tsige Real Madrid daga gasar Copa del Rey a wani wasa mai zafin gaske da suka fafata a filin wasa na Wander Metropolitano.


👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
Allah ya hada mu da alherin da Ke cikin wannan rana ta Juma a,Allah ya sa tausayin mu a zukatan shugabannin mu, Allah ya gafartawa iyayen mu,ya albarkaci iyalan mu. Ameen

------______Marubuci____
              Muhammad Auwal Suleiman
08153506684.

Zaku iya tallata kayayyakin ku ta kiran wannan lambar da Ke sama.

Comments

Popular posts from this blog

Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal