Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50
ASSALAM ALAIKUM
YAU LITNIN
10 GA RAJAB 1445
22--JANAIRU 2024
🇳🇬Nuhu Ribadu, Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro na Shugaba Bola Tinubu, ya gana da takwaran sa na gwamnatin Amurka, domin tattauna batutuwa na matsalar tsaro.
Cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Gwamnatin Amurka ta fitar a ranar Alhamis, ta ce Ribadu ya gana da Jake Sullivan, Mashawarcin Shugaban Amurka kan Harkokin Tsaro.
Tattaunawar ta su ta jiɓinci matsalar yadda za a daƙile ta’addanci da kuma muhimmancin kula da haƙƙin ɗan Adam.
Su biyun sun kuma tattauna babubutwa da suka jiɓinci ƙara wa dimokraɗiyya karsashi da kuma samar da nagartacciyar gwamnati a ƙasashen Afrika.
🧐Lambar tsohon gwamnan jihar Neja ta fito a wajen badaƙalar N4bn.
Hukumar EFCC ta maka tsohon gwamnan a gaban kotu kan zargin wawurar dukiya.
Hukumar ta kai shi kotun ɗaukaka ƙara bayan wata babbar kotu ta yanke hukuncin da ba ta gamsu da shi ba.
🏦Ministan tsaro, Muhammad Badaru, ya ya bawa magajin sa na jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi bisa ayyukan da ya faro Badaru, tsohon gwamnan na Jigawa ya ce a yanzu mutane sun gane gaskiyar abin da ya faɗa musu game da Ɗanmodi a lokacin kamfe Ya faɗi haka a ziyarar ya kai jihar wanda ake kyautata zaton ita ce ta farko tun bayan sauka daga mulki a watan Mayu.
Inda a lokaci ya dora harsashin Fara wash rukunin gidaje a unguwar Fanisau dake cikin garin Dutse babban birnin jihar.
🥹Jam’iyyar APC ta lashe zaben dukkanin kujerun ciyaman 27 da kansiloli 312 a Zaben Kananan Hukumomin Jihar Borno, da aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaban Hukumar Zabe na Jihar (BOSIEC), Alhaji Lawan Maina ne, ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben da aka gudanar ranar Lahadi a Maiduguri.
👾Kungiyoyin kwadago Najeriya na shirin yin fito-na -fito da gwamnatin kasar da na jihohi bisa rashin samun wani ci gaba a game da mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnati, kuma sun nuna cewa akwai yiwuwar yajin aiki.
Mataimakin magatakardan kungiyar kwadago ta NLC a kasar, Chris Onyeka, wanda ya bayyana haka, ya ce yanzu ma’aikata na cikin ukuba, inda ba sa iya biyan kudaden hayar gidajensu da ma kudaden makarantar ‘yayansu saboda matsanancin tsadar rayuwa.
👮🏻♂️Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce jami'an tsaro sun kubutar da 'yan matan nan biyar da ke hannun masu garkuwa da mutane bayan 'yan bindiga sun kashe 'yar'uwarsu wato Nabeeha Al-Kadriyar.
An sace 'yan matan shida ne da mahaifinsu ranar 2 ga watan Janairun da muke ciki a gidansu da ke Bwari a Abuja.
A sanarwar da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja Josephine Adeh ta fitar ranar Asabar da tsakar dare, ta ce jami'ansu da na rundunar sojin Nijeriya sun kubutar da ‘yan matan 'yan'uwan Nabeeha.
Sanarwar ta ce an gano su ne a kusa da dajin Kajuru da ke Kaduna ranar Asabar da misalin karfe 11:30 na dare.
Ta kara da cewa tuni aka kai 'yan matan gidansu da ke yankin Bwari a birnin na Abuja.
💀An kama wata mata da yunkurin Saida yara.
Rundunar yan sintiri ta vigilantee a Jihar Kano ta kama wata mata da ake zargin mai satar mutane ce a unguwar sharada dake nan Kano.
Matar dai ta yaudari wata mata da 'yayan ta 4, maza 2 mata 2 da niyyar zata kaita gidan wata mata da take bayar da taimakon kudi da kayan abinci.
Hakan ne tasa wasu yan vigilantee suka yi ta fakon ta har Allah ya basu Nasarar kama ta, wanda tuni tayi cinikin duk Namiji akan kuɗi Naira miliyan daya, mace kuma Naira dubu ɗari takwas.
Tuni dai suka mika matar da yaran da ta sato harda uwar 'yayan zuwa ga Rundunar 'yan sandan Kano domin fadada bincike a cewar Babban Kwamandan vigilantee na Jihar kano Alhaji Shehu Rabiu.
🐂Tsadar man fetur ta tilasta wa al'ummomi da dama a jihar Katsina sun koma amfani da 'amalanken shanu' wajen gudanar da harkokin sufuri.
🚑Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50 a ƙauyen Tse-Agubor Gyaruwa da ke gundumar Tsambee-Mbesev a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a jihar Benue. Shugaban ƙauyen da abin ya shafa, Cif Ayatse Agubor, ya shaida wa manema labarai a Makurdi cewa, gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Lahadi, yayin da mutanen ƙauyen ke aiki a gonakinsu.
Ya ce mahaifiyarsa ƴar 80 da gobarar ta kashe ba ta samu wanda zai taimaka mata daga gadon jinya ba saboda mutane ba sa gida a lokacin.
Agubor ya danganta gobarar da ƙona daji ba tare da izini ba, yana mai gargaɗin matasan ƙauyen da su guji aikata hakan ko kuma su fuskanci fushin hukuma.
🚗Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Kaduna, ta tabbatar da mutuwar mutum 16, yayin da wasu hudu suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Kano zuwa Kaduna.
Kwamandan hukumar a jihar, Kabir Nadabo ne, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a Kaduna.
A cewarsa, hatsarin ya auku ne a ranar Lahadi, a mahadar Taban Sani kusa da Tashar Yari da ke kan hanyar Kano zuwa Kaduna.
Nadabo ya ce, “Hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Toyota bas mai lamba TRB 674ZG, wadda ta taso daga Jihar Kano zuwa Jihar Benuwe.
“Mun aike da tawagar jami’anmu na Tashar Yari, inda suka kai dauki wajen da hatsarin ya auku.”
Ya ce binciken da aka gudanar, ya nuna cewar mutum 20 ne hatsarin ya rutsa da su, mutum 16 sun rasu sannan wasu hudu sun jikkata.
“An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Makarfi domin kula da su , yayin da aka kai gawar wadanda suka rasu zuwa Asibitin Koyarwa na ABU da ke Shika a Zariya.
Kwamandan hukumar, ya shawarci masu ababen hawa da su guji gudun wuce kima.
Ya ce hakan zai taimaka wajen tsira da rayuka ko dukiyoyin jama’a a duk lokacin da aka samu hatsari.
Kwamandan, ya ce FRSC na ci gaba da yin hadin gwiwa da sauran kungiyoyin sufuri wajen wayar da kan direbobinsu kan ka’idojin tuki, domin kaucewa hatsari.
DAGA KASASHEN WAJE
🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍
Wani sojan Isra’ila wanda bai jima da dawowa daga yaki a Gaza ba ya kashe abokinsa a Tel Aviv, kafafen watsa labaran Isra'ila sun ce akwai dubban sojojin kasar wadanda suka je yaki Gaza suka dawo da ke fuskantar matsalar kwakwalwa.
👥Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki Kwamitin Tsaro na Majalisar bisa rashin bai wa Afirka kujerar mamba ta dindindin a cikinsa.
🌍Wasu majiyoyi a Gabas ta Tsakiya sun ce kwamandojin rundunar juyin juye halin Iran da na Hezbollah suna Yemen, inda suke taimakawa wajen ba wa mayakan ‘yan tawayen Houthi umurni a hare-haren da suke kai wa jiragen ruwa a tekun Maliya.
LABARIN WASANNI
⚽⚽⚽⚽⚽⚽
⚽Maroko da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo sun yi kunnen doki a fafatawar da suka yi ranar Lahadi a gasar cin kofin nahiyar Afrika AFCON da ke gudana a Ivory Coast.
⚽'Yan wasan Nijeriya sun gudanar da atisaye a Abidjan gabanin karawar da za su yi da kasar Guinea-Bissau yau Litinin a ci gaba da gasar cin Kofin nahiyar Afirka
AFCON
-
🏐A cigaba da gasar Cin kofin kasashen Afrika kasar Afrika ta kudu ta lallasa kasar Namibia da ci 4 da 1
Inda kasashen Zambia da Tanzania suka ta Shi 1---1
------_-------------_-----------------
Allah ya hada mu alherin da yake cikin wannan rana ta Litinin...👏🏻
-----____----------______--------
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE
08153506684.
Allah ya sanya alheri
ReplyDelete