Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal

ASSALAM ALAIKUM
YAU LARABA
12 GA WATAN RAJAB 1445,DAI-DAI DA 24 GA WATAN JANAIRU 2024.

🇳🇬Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano a  yau Laraba, 24 ga watan Janairu, a gaban mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin almundahanar kudi har N4,008,573,350.

 Wakilinmu ya tattaro cewa a jiya Talata  za a gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kuliya bisa laifuka tara.

 Wannan ci gaban ya zo ne bayan mako guda da Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya sha alwashin sake duba duk wasu manyan laifuka da aka yi watsi da su, musamman wadanda suka shafi tsofaffin Gwamnoni da Ministoci.
🚙Ministan Birnin Taraya, Nyesom Wike, ya ce nan ba da da jimawa za a haramta wa maohtocin haya marasa fantin gwamnati aiki a birnin.

Wike ya shaida wa wani taron ’yan jarida a Abuja cewa yin hakan ya zama dole domin kawar da ayyukan masu motocin da ke yi wa fasinoji fashi, wadanda aka fi sani da ’yan ‘One Chance’ a birnin.

A cewarsa, duk da cewa ayyukan ’yan ‘One Chance’ sun ragu saosai, akwai bukatar daukar tsaruraran matakai domin kawo karshensu.

🇳🇬A jiya Talata 23 ga watan Junairu 2024 Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa karkashin jagorancin kwamishinan yansanda *CP AT ABDULLAHI, psc* ta shirya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya na zaben kujerar Dan majalisar wakilai Mai wakiltar Birnin kudu da Buji Wanda bai  kammala ba a wa su akwatuna a mazabar Birnin Kudu/ Buji zaben da Za a yi  a ranar Asabar 3 ga watan Fabrairu.  2024.

 Kwamishinan Zabe na jihar Jigawa, jami’an  rundunar ‘yan sanda, jami’in  baturen Yan Sanda  Birnin Kudu, Buji da Bamaina, da shugabannin jam’iyyar APC  da na jam’iyyar PDP ne suka halarci bikin.  .

 A karshe, CP ya sha alwashin yin taka tsan-tsan da duk wanda ke kokarin haifar da hargitsi kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.  Ya kuma tabbatar wa da jam’iyyu cewa ‘yan sanda ba su da hannu a ciki, kuma ba su da alaka da jam’iyya, kuma za su ci gaba da samar da filaye ga kowa a lokacin zabe.
 
🇳🇬Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita tsawon awa 24 a Karamar Hukumar Mangu nan take.Gwamna Caleb Mutfwang ya sanya dokar ce sakamakon ci gaban hare-hare da sauran matsalolin tsaro da suka yi ajalalin daruruwan mutane a karamar hukumar daga karshen shekarar da ta gabata.

Daraktan yada labaran gwamnan, Gyang Bere, ya sanar cewa, “Gwamna Mutfwang ya dauki matakin ne bayan ganawa da hukumomin tsaron da suka dace kuma dokar za ta ci gaba da aiki a karamar hukumar har sai abin da hali ya yi.”


🥸Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta tsige shugabanta, Olakunle Oluomo.

A safiyar Talata mutum 18 daga cikin mambobin 26 da ke majalisar suka kada kuri’ar amincewa da tsige Oluomo mai wakilatar mazabar Ifo.

Kafin tsige Oluomo dai ana zargin sa da karkatar da kudaden majalisar Naira biliyan 2.5.

Bayan tsige shi mambobin majalisar suka zabi Honorabul Elemide Oludaisi mai wakiltar mazabar Odeda a matsayin sabon shugaban majalisar.
⚖️Babbar Kotun Majistare da ke Kano ta tsare fitaccen dan siyasar nan, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda kan kalaman batanci da ya yi wa tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kotun dai ta tsare dan siyasar ne dangane da cin zarafin tsohon gwamnan na Kano, wanda a bayan nan ya ce dole ne a waiwayi batun raba Masarautar Kano da takwaransa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

Dangane da buƙatar neman beli ce kotun ta dage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar Litinin, 29 ga watan Janairu.
Bayanai sun ce kotun ta tura Dan Bilki Kwamanda ajiya a gidan kaso.


🎈Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal a birnin Damaturu na Jihar Yobe, ta lashe dukiya ta akalla Naira miliyan 150 a wannan Talatar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Damaturu, jami’in hulda da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Yobe, Malam Baba Bello, ya ce akalla shaguna 30 ne gobarar ta lalata.
Da misalin karfe 5:50 na safiyar Talatar, mun samu kiran gaggawa ana sanar da mu faruwar lamarin.

“Bayan ’yan mintuna kaɗan tawagar jami’anmu ta isa wurin, amma kafin isarta wutar ta riga ta yi karfi,” in ji Baba Bello.
🌚Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo, kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani a Jihar Nasarawa.

Bayanai sun ce an cafke Bodeje ne wannan Talatar a babban ofishin Miyetti Allah da ke Kasuwar Shanu a babbar hanyar Tudun Wada da ke Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasawara.
A ranar Laraba 17 ga watan Janairu Bello Badejo ya ƙaddamar da rundunar a garin Lafiya, inda ya ce za ta taimaka wajen yaƙar ɓarayi da ɓata-gari daga cikin Fulani

Wata majiyar DSS ta ce sun kama Bodejo ne kan fargabar cewa kirkiro da ƙungiyar sa-kai zai iya janyo tashin hankali a faɗin ƙasar, kuma kasancewar ba ta da rijista da hukumar ta DSS.


.
🌍DAGA KASASHEN WAJE 


Dakarun Hamas sun kashe sojojin Isra’ila 21 a harin kwanton-ɓauna, Hamas ɗin sun shammaci sojojin na Isra'ila inda suka harba musu makamin roka a tankar yaƙinsu a Gaza.

🌍Wani mahaifi ya harbe dansa har lahira saboda tutar jam’iyyar siyasa gabanin zaben kasar Pakistan da ke tafe.
Hukumomin ’yan sandan kasar sun ce mutumin da dan nasa sun samu sabani ne kan tutar jam’iyyar da za a sanya a jikin gidansu a kakar zaben.

Sun bayyana cewa dan, wanda kwanan nan ya dawo gida daga inda yake aiki a Qatar, ya sanya tutar Jam’iyyar PTI ta tsohon fira ministan Pakistan Imran Khan, a gidan nasu da ke yankin Peshawar da ke Lardain Khyber Pakhtunkhwa.

Amma sai mahaifin wanda kafin yanzu ya sanya tutar Jam’iyyar ANP a gidan, “ya haramta wa dan nasa sanya tutar PTI a gidan, amma duk da haka, dan ya ki sauke tutar ko daine goyon ban jam’iyyar
“Daga bisani lamarin ya yi zafi, inda cikin fushi mahaifin ya ciro karamar bindiga ya harbi dan dan nasa mai shekaru 31, sannan ya tsere daga gidan,” in ji wani jami’in dan sanda.

Jami’in ya bayyana cewa dan ya rasu ne a hanyar zuw asibiti kuma a halin yanzu an baza komar neman mahaifin.

A ranar 8 ga Fabrairun shekarar nan ta 2024 ne za a a gudanar da babben zaben kasar Pakistan mai cike da rikici, innda a lokuta da daman an kai hari kan masu takara a zaben.

🌍Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya isa Najeriya yayin da yake fara rangadin da yake yi a nahiyar Afirka.

 An shirya rangadin Blinken na Afirka tsakanin 21 ga Janairu zuwa 26, 2024.

 Ziyarar dai wani bangare ne na huldar da Amurka ke yi da kasashen Afirka, inda sakataren harkokin wajen kasar ke shirin tafiya Cabo Verde na kasar Cote d’Ivoire da kuma Angola bayan ya ziyarci Najeriya.
A yayin ziyarar Blinken, Ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar  zai yi shawarwari tsakanin kasashen biyu tare da mai da hankali kan zurfafa dimokaradiyya a yankin yammacin Afirka, da karfafa huldar kasuwanci da hadin gwiwar tsaro.

 Tuggar zai kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga Amurka da sauran al'ummomin duniya da su ba da la'akari sosai ga sauye-sauyen bangarori daban-daban, musamman ii tabbatar da dimokradiyyar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.


⚽FAGEN WASANNI ⚽

Tarzoma ta barke a Abidjan bayan mai masaukin baki Ivory Coast ta sha kashi a hannun tawagar Equatorial Guinea da ci 4-0 a wasansu na karshe na Rukunin A ranar Litinin da maraice.
Dubban magoya bayan kasar ne suka fice daga filin wasa kafin a kammala wasan. Wasu daga cikin ‘yan kasar Côte d'Ivoire da wasan bai yi wa dadi ba sun rika lalata ababen hawa.

⚽Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Afirka ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike kan wani faɗa da aka yi bayan wasan da aka yi tsakanin DRC da Maroko inda ƴan wasa da jami’an kwallon ƙafa suka shiga rikicin.
Lamarin ya faru ne jim kadan bayan kammala wasan  Inda kaftin din DRC chancel mbemba da kocin Motoko Walid suka Fara fada. Rikicin ya haifar da cece-kuce tsakanin 'yan wasa da jami'an kungiyoyin biyu da suka ci gaba da barin filin.

⚽A hukumance: Najeriya za ta kara da Kamaru a wasa nagaba na gasar #AFCON2023 zagaye na 16 a ranar Asabar.


🏐Mauritania 🇲🇷 1-0 Algeria 🇩🇿 

Algeria ta fice daga gasar AFCON a mataki na Rukuni karo na biyu a jere! 

🏐Angola ta zama ta ɗaya a rukunin D bayan ta doke Burkina Faso, Wadda ta kasance ta biyu a rukunin.Bayan da suka ya Shi Angola 2 Burkina Faso 0
---_---_-_-'-'-_-_---_-------__--__----+
Allah ya hada mu da alherin wannan rana ta Laraba""Ta bawa ranar Samu".Allah ya tsare mu daga  sharrin wannan Zamani..Allah yasa mu yini lafiya.
--__---------_---_---------_---_-
MARUBUCI
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE
08153506684.

Comments

Popular posts from this blog

Kotun kolin kasar nan ta sanya yau Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar

Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50