Akalla mutane uku ne ake fargabar sun rasa rayukansu a wani rikici da ya kaure tsakanin baban bola da mutanen


ASSALAM ALAIKUM 

YAU ALHAMIS 

09 GA ZUL QIDAH 1445

16 GA MAYU 2024
🇳🇬Bola Tinubu ya gana da Gwamna Ahmed Ododo a Villa ranar Laraba.

Gwamnan ya yi wa shugaban ƙasar bayani kan abubuwan da ke faruwa a jiharsa musamman kan tsaro.

Tinubu ya yabawa gwamnan bisa ƙoƙarin da ya yi bayan sace ɗaliban jami'ar kimiyya da fasaha.

🇳🇬Wasu yan majalisar dokokin Najeriya sun fara yunkurin kawo sauyi a tsarin mulkin da ake bi a tarayyar Najeriya Yan majalisar sun kai ziyara ga Obasanjo domin neman goyon baya kan sabon aikin da suka dauka na canja tsarin mulkin Obasanjo ya karbi korafin yan majalisar ya kuma lissafa musu abubuwan da ya kamata su mayar da hankali a kai yayin aikin
🇳🇬Hukumar Kula da Ɗanyen Mai Da Ake Fitarwa Waje (NUPRC), ta bayyana cewa an fara bayar da lasisin mallakar rijiyoyin mai na shekarar 2024.

Shugaban Hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe ne ya bayyana haka a Miami, Florida a ƙasar Amurika inda hukumar ta ɗauki nauyin wani nune-nune, tare da haɗin-gwiwar Kungiyar Masu Fasahar Harkokin Ɗanyen Mai ta Najeriya (PETAN).

Hukumar ta ce rabon lasisin mallakar rijiyoyin ɗanyen mai a 2024 zai shafe tsawon watanni 9.

🇳🇬Darajar Naira na ci gaba da faɗuwa a farashin gwamnati da kuma kasuwar ‘yan canji a ranar Talata.

Ƙididdigar alƙaluman canjin kuɗin da wannan jarida ta bi diddigi ya nuna cewa a ranar Talata an sayar da Dalar Amurka 1 kan Naira 1,520.

Darajar Naira ta faɗi idan aka yi la’akari da cewa a ranar Litinin an sayar da Dala 1 kan Naira 1,478.11.

Farashin ranar Talata ya nuna cewa Dala ta ƙara daraja da Naira 42.29, ita kuwa Naira, darajar ta ce ta ragu da Naira 42.29.


🇳🇬🇳🇬Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin dakatar da kwamitocin bincike da gwamnatin jihar ta kafa domin binciken gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ne gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da kwamitocin shari’a guda biyu da suke gudanar da bincike kan almubazzaranci da dukiyar jama’a, tashe-tashen hankulan siyasa da kuma bacewar mutane tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023.
🇳🇬Hukumar Zaɓen Jihar Yobe (SIEC) ta sanar da ɗage zaɓen ƙananan hukumomin da ta shirya gudanarwa a ranar 25 ga Mayun 2024.

Hukumar ta ce ta ɗage zaɓen zuwa ranar Asabar, 8 ga watan Yunin bana kuma a wannan rana yaƙin neman zaɓe ya ƙare kamar yadda ka’idojin zaɓen suka tanadar.

🇳🇬Ƙarin wasu kwamishinoni uku sun ajiye aikinsu yayin da suka miƙa takardun murabus daga Majalisar Zartarwa ta Jihar Ribas.

Kwamishinoni sun haɗa da na ilimi, Farfesa Chinedu Mmon, da na gidaje, Gift Worlu da kuma na muhalli, Austin Ben Chioma.
Bayanai sun ce kwamishinonin sun ajiye muƙamansu saboda abin da suka kira “hatsarin da ke cikin ayyukansu.”

Kwamishinonin waɗanda masu biyayya ne ga tsohon gwamnan jigar, Nyesom Wike
🇳🇬Hukumar Kwastam ta sanar da samun nasarar kama man fetur da darajarsa ta kai kusan Naira miliyan 8.85 daga hannun masu fasa ƙwauri a Legas a yayin da ake fama da ƙarancinsa a ƙasar.

A cewar Kwanturola Paul Bamisaiye, kwamandan hukumar ta Kwastam na shiyyar Yamma, an tsananta sintiri a magudanan ruwa a Legas, lamarin da ya sa aka kama man fetur ɗin da aka yi fasa ƙwaurinsa, wanda ake daf da ƙetarewa da shi zuwa Jamhuriyar Benin.
🇳🇬Sakataren zartarwa hukumar Kula Da Asibitocin Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya amince da dakatar da wata likita a Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase bisa zarginmta da yin watsi da marasa lafiya.

Wannan dai ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da majiyyata da ma’aikatan asibitin da aka samu bayan likitar ta bar wurin marasa lafiyan ba tare da sanar da mahukuntan asibitin ba.
Ya bayyana cewa, an yi mata kiraye-kirayen da yawa amma ta ci gaba da cewa tana asibiti alhalin ba ta taɓa zuwa ba, wanda hakan ya sa majinyacin mai fama da cutar ƙoda a cikin wani mummunan hali.

🇳🇬Shugabannin jam'iyyar APC mata a jihohin kasar nan 36 sun nuna bakin cikin yadda gwamnatin Bola Tinubu ta yi watsi da su Shugabar matan, Misis Patricia Yakubu da ta jagoranci gangamin nuna goyon baya ga Dr. Abdullahi Umar Ganduje ce ta bayyana hakan Ta ce tun da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kama aiki, turmin atamfa daya da buhun shinkafa ne kawai ya ratsa tsakaninsu da jam'iyyar.

🇳🇬Limaman Masallatan juma'a a Jihar Neja dake Najeriya sun sha alwashin ci gaba da shirin aurar da yara marayu mata guda 100 da Kakakin majalisar dokokin jihar ya shirya yi, kafin daga bisani ya janye, yayin da suka bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta korar ministan kula da harkokin mata daga kujerar ta saboda abinda ta kira rashin iya aiki da kuma yunkurin haifar da rikicin addini a Najeriya.
🇳🇬Wasu ƙarin mutum bakwai daga cikin waɗanda suka samu rauni a harin masallaci a jihar Kano sun riga mu gidan gaskiya Hakan ya sa adadin waɗanda suka mutu a harin ya zama mutum takwas yayin da sauran mutane 17 ke kwance a asibitin Murtala Muhammad Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano.

Matashin da ake zargi mai suna Shari’u Abubakar, mai shekaru shekaru 38, ya ce shi ne ya sayo fetur ya cunna wutar inda ya wurga ta a cikin masallacin, lamarin da ya sa mutane da dama suka ƙone sassan jikin su.

“Aƙalla mutane 24 ne suka ƙone bayan da matashin ya kunna musu wuta a cikin masallacin, wanda tuni jami’an mu suka kai su Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, inda suke ci gaba da samun kulawar likitoci, “in ji SP Kiyawa”.

🇳🇬Akalla mutane uku ne ake fargabar sun rasa rayukansu a wani rikici da ya kaure tsakanin baban bola da mutanen da ke zaune a Kubwa da a Abuja Rigimar ta samo asali ne bayan an yi zargin wani baban bola da yunkurin dauke tukunyar wata mata mazauniyar unguwar Byazhin Bayan ta nemi daukin makwabta ne aka dakile yunkurin baban bolan, shi kuma sai ya tattaro yan abokansa su ka dawo da makamai

DAGA ƘASASHEN WAJE 
🌍An jikkata firaiministan Slovakia, Robert Fico sakamakon harbin bindiga kamar yadda rahotanni ke cewa.

Rahotanni dai sun ce an harbi mista Fico a ƙofar cibiyar baje al'adun gargajiyar ƙasar da ke garin Handlova, inda ake gudanar da wani taron gwamnatin.

'Yan jarida sun rawaito cewa an ji ƙarar harbe-harbe.

🌍Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugabannin kasashen Amurka da Faransa sun bayyana kaduwar su a kan yadda wani 'dan bindiga ya dirkawa Firaministan Slovak Roberto Fico harsasai a cikin sa. Mai magana da yawun gwamnatin Slovak Zuzana Caputova tace tuni aka kama 'dan bindigar, yayin da aka ce Fico na cikin mawuyacin hali.

🌍Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, reshen Al Qassam Brigades, ta sanar da cewa, ta kashe sojojin Isra'ila 12 a yankin Arewacin Gaza da aka yi wa ƙawanya.

🇳🇬Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasa Donald Trump sun amince su tafka mahawara ta talabijin ranar 27 ga watan Yuni dangane da halin da kasar su ke ciki gabanin shirin zabe mai zuwa.

..,................----------___
Allah ya haɗa mu da alherin wannan rana ta Alhamis.Allah ya gafarta mana mu da iyayen mu.
-------------.........-------
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE

Comments

Popular posts from this blog

Kotun kolin kasar nan ta sanya yau Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar

Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal