Akwai yiyuwar cewar akalla ‘yan Najeriya miliyan 32 ne zasu fuskanci wani yanayi mai kama da matsananciyar yunwa.
ASSALAM ALAIKUM
YAU JUMA A
2 GA ZUL QIDAH 1445
10 GA AFRILU 2024
🇳🇬Majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙudurin dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar, bayan ƙudurin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar.
Majalisar ta amince ta ƙudurin bayan kwamitin majalisar kan ayyukan yaƙi da fataucin miyagun ƙwayyoyi, ƙarƙashin jagorancin Sanata Tahir Munguno ya gabatar da rahotonsa kan sabuwar dokar a zauren majalisar.
Yayin da take sake nazarin dokar, majalisar ta amince da dokar hukuncin kisan ne domin ƙarfafa ayyukan hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar.
A lokacin muhuwar, babban mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Peter Nwebonyi ya nemi majalisar ta amince da dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyin, maimakon ɗaurin rai -da-rai.
A lokacin da aka nemi ra'ayin sauran 'yan majalisar dangane da batun, majalisar ta nuna amincewarta kan dokar ciki har da mataimakin shugaban majalisar dattawan ƙasar.
To sai dai wasu tsirarun 'yan majalisar ba su goyi bayan ƙudurin ba, inda Sanata Adams Oshimole ya kasance cikin masu nuna adawa da dokar.
To sai dai mataimakin shugaban majalisar dattawan, Sanata Barau Jibril ya yi watsi da buƙatar sanata Oshimolen, yana mai cewa ƙorafin sanatan ya saɓa wa dokar majalisar saboda ƙorafin ya zo ne bayan majalisar ta amince da ƙudurin.
🇳🇬Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya ziyarci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a fadar sa dake Birnin Tarayya Abuja Villa.
Uba Sani, ya ce ya ziyarci Shugaban ne domin sanar da shi irin ci gaban da ake samu a jihar ta fuskar tsaro da ci gaban bil’adama.
Gwamnan yayi kuma amfani da wannan dama wajen mika godiyar sa ga mai girma shugaban kasa bisa jajircewarsa na ganin an gaggauta kammala aikin titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, Wanda Titin Bypass ya ratso da aikin titin Mandozuwa Birnin Gwari da kuma titin Kafanchan zuwa Kwoi.
Sanata Uba Sani, ya ce Shugaba Tinubu yi alkawarin baiwa Jihar Kaduna dukkan goyon bayan da ake bukata don daidaita jihar Kaduna da magance manyan kalubalen da muke fuskanta na bangaren cigaba gaba.
🇳🇬ICPC ta gurfanar da kwamandan NSCDC bisa zamba cikin aminci.
Kwamandan mai suna Christopher Oluchukwu ya karbi kudade a wurin mutane da dama domin sama musu aiki.
Lauyan ICPC ya bayyana hakan a matsayin laifi da ya sabawa dokar kasa.
🇳🇬Rikici siyasa ya kara ƙamari a jihar Rivers yayin da yan majlisa ke kokarin tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara Babban jigo a jam'iyyar PDP, Sanata Adolphus Wabara ya yi kira na musamman ga shugaba Bola Tinubu kan shiga lamarin Sanata Adolphus Wabara ya bayyana irin hatsarin da rikicin zai haifar da kuma yadda zai shafi Najeriya baki daya.
🇳🇬Yarima Harry da uwargidansa Meghan zasu fara ziyarar aiki ta kwanaki 3 a Najeriya daga yau juma'a. Ma'aikatar tsaron kasar tace Yariman zai ziyarci sojojin Najeriyar da suka samu raunuka wajen yaki da 'yan ta'adda a asibiti domin basu kwarin gwuiwar ayyukan da suke yi.
🇳🇬Kotu a Kano ta sanya ranar fara sauraren shari'ar da shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya shigar gabanta.
Shugaban yana neman kotu ta soke korarsa da wasu 'yan jam'iyyar suka yi.
Yana ganin korar ta wasu ke kokarin yi ya saba da 'yancinsa na dan Adam..
🇳🇬Ƙungiyar kare haƙƙin ’ƴan ƙasa da tabbatar da shugabanci na gari (SERAP) ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya janye harajin tura kudi ta intanet da ya ɗora wa ’yan kasar.
SEEAP ta ce harajin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa.
🇳🇬Akwai yiyuwar cewar akalla ‘yan Najeriya miliyan 32 ne zasu fuskanci wani yanayi mai kama da matsananciyar yunwa a tsakanin watanin Yuni da Agustar shekarar da muke ciki matukar ba’a dauki matakan gaggawa ba, a cewar rahoton Cadre Harminise’ na baya-bayan nan, wanda kwamitin kai dauki na kasa da kasa da gwamman kungiyoyin kasa dake aiki a yankin suka wallafa.
A cewar rahoton, adadin mutanen da zasu fuskanci matsalar karancin abinci a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar afirka a wannan dan tsakani zai kai kimanin mutane milyan 52 kwatankwacin kaso 12 cikin 100 na mutanen da aka tantance.
🇳🇬Wani mutum mai shekaru 40 ya aika matarsa lahira saboda za ta je ganin danta a gidan mininta na fari.
Magidancin ya caka wa matar tasa almakashi ne a yayin gardamar da ta barke a tsakaninsu bayan daukar dogon lokaci suna zaman doya da manja.
Makwabtantan ma’aratan da ke zaune a garin Akure a Jihar Ondo sun shaida wa wakilinmu cewa, sun sha yi musu sulhu amma abin ya ci tura.
Daya daga cikin makwabtan ya ce, “Abin takaici ne a ce ya kashe matarsa. Mun sha yi musu gargadi game da yawan fadan da suke yi tsakaninsu amma ba su bari ba
🇳🇬Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Sadiq Zubairu, bisa zargin kisan abokinsa Bello Bukar Adam wanda ma'aikacin kamfanin rarraba wutar lantarki ta KEDCO ne.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya ce a ranar 5 ga watan Mayu ne rundunar 'yan sanda ta samu ƙorafin ɓatan Bello Bukar Adam mai shekara 45, wanda aka ce ya bar gida tun ranar 4 ga watan Mayun.
Sanarwar ta ce a ranar ne kuma 'yan sanda suka samu rahoton tsintar gawar mutumin, wanda aka jefar a ƙauyen Bechi da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso, inda nan take rundunar 'yan sanda ta tura tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin DPO na ƙaramar hukumar, inda suka ɗauko gawar zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Inda nan take rundunar 'yan sanda ta ƙaddamar da bincike tare da kama wani mutum mai suna Sadiq Zubairu mai shekara 35 da ke unguwar Hotoron Arewa bisa zargin aikata laifin.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce a lokacin da 'yan sandar ke tuhumar wanda ake zargin, ya amsa cewa ya haɗa baki da wasu mutum biyu wajen fito da Bello - wanda ya kasance abokinsa ne - daga gidansa.
Sadiq ya shaida wa 'yan sanda cewa da kansa ya ɗaure Bello inda suka rika dukansa da sanduna da ƙarafa masu kaifi a kansa da sauran sassan jikinsa har sai da ya mutu.
''Bayan ya mutu ne suka sanya shi jikin but ɗin motarsa, tare da jefar da gawar a kan titin Eastern Bypass, a daidai ƙauyen Bechi, inda suka gudu da motar, ƙirar Toyota Corolla 2015, da kuma wayar marigayin'', kamar yadda sanarwar 'yan sandan ta yi bayani.
DAGA ƘASASHEN WAJE
🌍Sakamakon farko-farko da Hukumar zaɓe ta fitar ya nuna cewa Deby ya cinye kashi 61 na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da babban abokin hamayya kuma Firaminista Succes Masra ya zo na biyu da kashi 18.5.
🌍🗞️ Firaiminista Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Alhamis cewa barazanar da Amurka ta yi na hana makamai ba za ta hana Isra’ila ci gaba da kai hare-hare Gaza ba, lamarin da ke nuni da cewa za ta iya yin gaban kanta wajen mamaye birnin Rafah mai cunkoson jama’a ba tare da goyon bayan babbar kawarta ba.
🌍Fitacciyar tauraruwar fina-finan batsa ta Amurka, Stormy Daniels ta yi musayar kalamai da tawagar lauyoyin Donald Trump, a lokacin da ta ke bayar da shaida a shari'ar da ake wa tshohon shugaban kasar na aikata laifuka a New York.
Tsohon shugaban na Amurka ya musanta yin ƙarya a bayanan kasuwanci don ɓoye kuɗin toshiyar baki da aka biya Ms Daniels kan alaƙar da ta shiga tsakaninsu a 2006.
Donald Triump ya daɗe yana musanta yin lalata da Stormy Daniels, kuma a yau lauyansa ya nemi ya warware duk shaidar da ta bayar inda ya zarge ta kai-tsaye da kitsa labarin ƙanzon kurege.
FAGEN WASANNI
😭Tsohon ɗan ƙwallon Super Eagles ta Najeriya, Tijjani Babangida, ya yi hatsari a mota inda ƙaninsa Ibrahim ya rasu nan take.
Tsofaffin ‘yan kwallon sun yi hatsari ne a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya. Yanzu haka Tijjani da matarsa Maryam Waziri suna asibiti suna samun kulawar likitoci.
🏐Zakarun na Jamus sun samu gurbi a wasan ƙarshe na Gasar Europa League bayan canjaras 2-2 da suka yi da Roma, wato 4-2 jimilla, kuma za su kara da Atalanta a wasan ƙarshen.
Leverkusen dai ta sha tsallake rijiya da baya a ƙarshen wasanni da dama cikin wannan kakar.
-------------------------
Allah ya hada mu da alherin da Ke cikin wannan rana ta Juma a,Allah ya sa tausayin mu a zukatan shugabannin mu, Allah ya gafartawa iyayen mu,ya albarkaci iyalan mu. Ameen
------______Marubuci____
Muhammad Auwal Suleiman
Comments
Post a Comment