Kotu ta daure wata matar aure ’yar shekara 28 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba, kan laifin zuba wa kishiyarta ruwan zafi da gangan a lokacin da kishiyar take tsaka da barci.


AS-SALAM ALAIKUM 

YAU ASABAR 

3 GA ZUL QIDAH 1445

11 GA AFRILU 2024

🇳🇬Majalisar ta umarci CBN ta kuma umarci CBN ya gagguta janye umarnin da ya ba wa bankuna na cirar harajin na kaso 0.5% daga kudaden da aka tura ta na’urorin zamani.
U
Umarnin majalisar na zuwa ne bayan koke da kakkausar suka da sabuwar dokar ta CBN ke sha daga ’yan Najeriya da kanfanoni da masana da ma kungiyoyi
🇳🇬Wasu 'yan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da ɗaliban jami'a tara a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.

Sai dai ana fargabar adadin zai iya zarta hakan.

Rahotonni sun ce maharan sun dirar wa jami'ar Confluence University of Science and Technology ne da ke Osara–Okene da tsakar dare ranar Alhamis.

Bayan sun isa ne kuma suka dinga shiga ɗakunan ɗaliban da ke karatu domin shirya wa jarabawar da ke tafe kuma suka buɗe wuta a sama, suka tara wasu ɗalibai kuma suka wuce da su.

🇳🇬Kotu ta hana ƴan majalisa 27 bayyana kansu a matsayin mambobin majalisar dokokin Ribas.

Alkalin kotun ya hana ƴan majalisar yin aiki daga nan har sai kotun ta yanke hukunci.

Ƴan majalisar da matakin ya shafa sune suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
.
🇳🇬Majalisar Dattawa ta amince da kudirin karin albashi ga ma'aikatan shari'a a Najeriya yayin da ake cikin wani halin matsi Kudirin da aka gabatar a gaban Majalisar ya tsallake karatu na biyu inda shugaban alkalai zai samu albashin N5.38m a wata Sanata Ashiru Yisa daga jihar Kwara ne ya gabatar da kudirin a gaban Majalisar kan inganta albashi da alawus na ma'aikatan.
..🇳🇬Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki (KEDCO) ya yi albishir ga abokan huldarsa dake jihohin Arewa uku da cewa za a samu karuwar hasken wuta Kamfanin ya ce zai samar da Karin 40MW na hasken wuta cikin watanni 18 a jihohin 3 na Kano da Jigawa da Katsina da kuma aiki, kuma yana aiki da gwamnoni Haka kuma za a bullo da sabbabbin hanyoyin biyan kudin wuta domin dakile karkatar da kudin da ake kara daga abokan huldar kamfanin

🇳🇬Hukumar kwastam ta sanar da kama na'urorin kirifto da makamai a jihar Lagos. 

Kwamandan hukumar ne ya bayyana haka yayin da yake lissafa abubuwan da suka kama cikin watanni 4. 

Ya kuma bayyana yadda suka yi da kayayyakin kamar yadda aka umurce su.
.🇳🇬Babban Bankin Duniya (WB) ya bayyana shirin raba tallafi na musamman na N5000 ga talakawan kasar nan bai yi amfanin komai ba Wannan na kunshe cikin rahoton da babban bankin kasar nan CBN ya fitar mai taken “tasirin raba tallafin kudi ga mata da gidaje a Najeriya Bankin duniya ya bayyana cewa babu 
wasu alkaluma da suka tabbatar da ikirarin gwamnatin tarayya na cewa an samu nasara sosai wajen raba tallafin 
🇳🇬Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana ayyukan alheri da ya kawo Najeriya.

Jonathan ya koka kan yadda aka lalata dukkan abubuwan alheri da ya kawo bayan barin mulki.

Ya bukaci a ba mata dukkan dama da suke bukata ba tare nuna musu wariya ba.
🇳🇬🇳🇬Gwamnatin Jihar Jigawa ta na ƙulla haɗin gwiwa da Bankin Bunƙasa Ƙasashen Afrika (AfDB), domin ganin an raya Rukunin Masana’antun Bunƙasa Harkokin Noma (SAPZ) da ke Gagarawa.

Gwamnatin ta sanar haka a lokacin da tawagar manyan jami’an Bankin AfDB suka kai wa Gwamna Umar Namadi ziyara, ƙarƙashin jagorancin Monde Nyambe, a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Dutse.
🇳🇬🇳🇬Allah ya yi wa ɗan Majalisar Wakilan Nijeriya Hon. Isa Dogonyaro rasuwa jiya Juma’a. Marigayin shi ne yake wakiltar mazaɓar Garki da Babura daga jihar Jigawa a Majalisar Wakilan Nijeriya.
Wata sanarwa da shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar Akin Rotimi ya fitar ta ce marigayin ya rasu ne da safiyar Juma’a a Abuja, yana da shekara 46.
Sanarwar ta ce Hon. Isa ya bar mata da ‘ya’ya.
An yi jana’izarsa a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja, bayan sallar Juma’a.

🇳🇬Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Tikau, Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema rasuwa a ranar Juma’a.

Rasuwar sarkin mai daraja ta ɗaya ta jefa al’ummar Sabon Garin Nangere da ke Karamar Hukumar Nangere cikin ruɗani kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

Wata majiya da ke kusa da fadar Tikau ta ce, Sarkin ya rasu ne a Asibitin Kwararru na garin Potiskum bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Majiyar ta ce sai nan gaba kadan za a sanar da cikakkun bayanai game da jana’izar marigayi sarkin na Tikau.



🇳🇬Kotu  ta daure wata matar aure ’yar shekara 28 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba, kan laifin zuba wa kishiyarta ruwan zafi da gangan a lokacin da kishiyar take tsaka da barci.

Babbar Kotun Majistare da ke Gwagwalada a Abuja ta yanke wa matar da ke zaune a kauyen Gosa Toge hukuncin ne bayan an gurfanar da ita kan zargin aikata laifukan cin zarafi da kuma cutar da dan Adam.

Babban alkalin Kotun, N.A Turkur, da ya yanke mata hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni takwas ba tare da zabin biyan tara ba, ya gargade ta da ta daina aikata irin wannan aika-aikar, kuma ta kasance mai kyawawan halaye.

DAGA ƘASASHEN WAJE 

🌍Ɗaya daga cikin manyan gidajen burodi mafi shahara a Japan na ƙoƙarin dawo da dubban sunƙin burodin da ya sayar tare da mayar wa waɗanda suka saya kuɗinsu bayan an tsinci wani ɓangare na jikin ɓera a wasu burodin da ya sayar.

Kimanin burodi sunƙi 104,000 na gidan burodin Pasco Shikishima ne aka cire daga kantuna sanadiyyar al'amarin.

An ga wani ɓangare na jikin ɓera a cikin ƙunshin burodi aƙalla biyu.

Akasarin iyalai a Japan na amfani da burodin na kamfanin Pasco, sannan burodi ne da ake iya gani a kusan kowane kanti da ke faɗin ƙasar.

Ya zuwa yanzu dai babu rahoton wani da za a ce ya kamu da rashin lafiya sanadiyyar cin burodin, kamar yadda kamfanin burodin ya sanar..
.
🇳🇬Shauki ya sa wata maniyyaciyar hajjin bana ‘yar kasar Indonisiya ta yi Sujjada a lokacin da jirginsu ya sauka a birnin Madinah domin Hajjin Bana.

Maniyyaciyar ta ce tayi wa Allah godiya da ya kawo ta ƙasar Saudiyya don sauke farali a Wannan Shekara.

FAGEN WASANNI 
⚽⚽Zuwa yanzu, alamu duka sun nuna cewa a kakar wasa mai zuwa, Osimhen ya zaɓi buga wasa a gasar Firimiya ta Ingila, maimakon gasar League 1 ta Faransa, duk da a baya ya taɓa buga wa ƙungiyar Lille ta Faransar kafin tafiyarsa Napoli.
⚽Ba tabbas a game da makomar dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson a Ajax bayan da Kungiyar ta kasa tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasanni na biyu a jere
............-----------.......

Allah ya yaye mana dukkanin matsalolin day Suka addabe mu,ya gafarta mana,ya albarkaci Zuri ar mu,ya sanya alherin sa a gidajen mu.
...............----------
MARUBUCI MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE

Comments

Popular posts from this blog

Kotun kolin kasar nan ta sanya yau Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar

Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal