Hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta gayyaci tsohon gwamnan Kano kan zamba An gayyaci Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso domin bayar da bayanai


ASSALAM ALAIKUM 

YAU ASABAR

24 GA ZUL QIDAH 1445

1 GA Yuni 2024



 *TAKAITATTUN LABARAN* 

🇳🇬Asusun bayar da bashin karatu na Najeriya (NELFUND) ya ce sama da ɗalibai miliyan 9.5 ne suka kai ziyara ofishinta dangane da bashin karatu da za a bai wa dalibai tun bayan buɗe shafin da za a cike takardar neman bashin karatun a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sama da ɗalibai 6,000 ne suka cike takardan neman bashin.

Yayin da yake yi wa manema labarai karin haske a taron da aka shirya wa ɗaliban da suka cike takardan neman bashin a ranar Alhamis, shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce sama da kashi 90 cikin 100 na manyan makarantun gwamnatin tarayya sun mika bayanan dalibansu da cibiyoyi kusan biyar da suka rage


🇳🇬Yayin da ake tsaka da rikicin masarautun Kano, shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya roki ƴan Najeriya kan mulkin Bola Tinubu Ganduje ya ce tun yanzu tsare-tsaren da Tinubu ke dauka sun fara haifar da ɗa mai ido a cikin shekara daya da ya yi kan mulki Shugaban jam'iyyar APC na kasa ya bayyana haka ne yayin kaddamar da littafin cika Tinubu kwanaki 365 a kan mulkin Najeriya 

🇳🇬Rahotanni na bayyana cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta gayyaci tsohon gwamnan Kano kan zamba An gayyaci Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso domin bayar da bayanai kan zargin da ake yi masa na almundahanar kudin 'yan fansho Amma babban mai ba gwamnan Kano shawara kan kafafen yada labarai Bashir Sanata ya shaidawa Legit cewa duk bita da kullin siyasa ce kawai.
🇳🇬Wata kungiyar lauyoyi ta fara shirin maka shugaba Tinubu da 'yan majalisa gaban kotu.

Kungiyar ta zargi shugaban da ‘yan majalisa da sauya taken Najeriya ba bisa ka’ida ba.

Sakataren kungiyar Tonye Jaja ya ce an saba dokokin kasar nan da dama wajen canja taken.

🇳🇬Shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya Nigerian Bar Association (NBA) ya ce za su binciki lauyoyin ɓangarorin da ke jayayya da juna a rikicin masarautar Kano da ke arewacin ƙasar.

Cikin wata sanarwa, Yakubu Chonoko Maikyau ya kuma nemi hukumar kula da harkokin shari'a ta ƙasa (NJC) ta binciki alƙalan da suka ba da umarni masu karo da juna kan rikicin masarautar.

Tun da farko wata babbar kotun tarayya ta nemi a dakata da sauke Sarki Aminu Ado ko sauya dokar masarautun Kano har sai ta kammala sauraron ƙorafin da aka kai mata. Daga baya kuma wata babbar kotun Kano ta ba da umarnin kare Sarki Muhammadu Sanusi II kuma ta yi gargaɗin kada a fitar da shi daga gidan sarauta.

Bugu da ƙari, babbar kotun ta Kano ta sake ba da umarnin bai wa Aminu Ado kariya da kuma gargaɗin kada a fitar da shi daga gidan sarauta. Sanusi na zaman fada a fadar Gidan Rumfa, yayin da Aminu ke nasa zaman a gidan sarki na Nassarawa.

Ya ce abin da lauyoyin suka yi "ya jawo ƙasƙanci" ga ayyukansu kuma "za a ɗauki tsawon lokaci kafin a manta da irin abin kunyar da suka jawo

DAGA ƘASASHEN WAJE 

🌍Kotu ta
 kama tsohon shugaban Amurka Donald Trump da aikata wasu mugayen laifuka.

Laifukan sun hada da boye bayanan kasuwancinsa da bayar da toshiyar baki.

Tambayar da ke ran masu bibiyar siyasa ita ce ko mista Trump zai iya tsayawa takara.


🌍Kakakin majalisar Iran har sau uku kuma tsohon mai shiga tsakani kan harkokin nukiliya, Ali Larijani, ya yi rijistar shiga takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.

Akwai bukatar majalisar amintattun kasar ta sahale wa takarar tasa, wadda a baya ta hana shi shiga takarar.

Mista Larijani - wanda mai matsakaicin ra'ayi ne - ya yi alƙawarin farfado da tattalin arzikin Iran.

Kawo yanzu saura makoi hudu a yi zaɓen kasar.

An dai matso da zaɓen ne sakamakon mutuwar tsohon shugaban ƙasar Ibrahim Rasi a haɗarin jrgin sama.


🌍Jami'an tsaron Faransa sun ce sun dakile wani hari da aka shirya kai wa a birnin Paris lokacin wasan Olympics a ƙarshen watan Yuli.

Ministan cikin gidan ƙasar ya ce wani yaro dan shekara 18 da aka kama a farkon watannan dan yankin Chechenya, ake zargi da shirya kai harin a filin wasan kwalon kafa na St Etienne.

Idanuwan Faransa a buɗe suke a yayin wasannan Olympics din, wanda miliyoyin mutane za su halarta domin kallo.

🌍Falasɗinawa sun soma komawa gidajensu a birnin Jabalia na Gaza yayin da dakarun Isra'ila suka janye daga yankin ranar 30 ga watan Mayu, bayan sun kwashe kusan mako uku suna luguden wuta inda suka yi rugu-rugu da yankin.

Duk da ƙwarya-ƙwaryar janyewar da dakarun Isra'ila suka yi, wani kwamitin gaggawa na yankin ya gargarɗi mutane da kada su koma wasu unguwanni domin kuwa Isra'ila na amfani da jirage marasa matuƙa don kai hari kan mutanen da ke yunƙurin komawa gidajensu.

Wasu ganau sun shaida wa kamfanin labarai na Anadolu Agency cewa jirage marasa matuƙa na Isra'ila na kai hari kan mutanen da ke neman mafaka a makarantar Falasteen  da ke Jabalia, inda suke kashewa tare da jikkata gomman jama'a

DAGA FAGEN WASANNI 


⚽Kyaftin din tawagar kungiyar kwallon kafa ta kasar Faransa, wanda kwantiraginsa zai kare a ranar 30 ga watan Yuni tsakaninsa da Paris Saint-Germain(PSG),ya yanke shawarar komawa Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bayan shafe shekaru bakwai a PSG.
---------------------

Allah ya haɗa mu da alherin wannan rana ta Talata.Allah ya gafarta mana mu da iyayen mu.
-------------.........-------
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN

Comments

Popular posts from this blog

Kotun kolin kasar nan ta sanya yau Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar

Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal