Aƙalla mutane 42 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ƙyanda
ASSALAM ALAIKUM
YAU LAHADI
26GA SHAWWAL 1445
5 GA MAYU 2024
🇳🇬🇳🇬Karfin tattalin arzikin Legas ya kai N41tr, wannan ya ninka arzikin jihar Yobe sama da sau 40 kenan.
Ribas, Akwa Ibom, Delta da Bayelsa da suke da arzikin danyen mai suna cikin jihohin da suka fi kudi.
Idan ana zancen karfin tattalin arziki a Najeriya, Borno, Nasarawa, Kebbi da Zamfara suna sahun baya.
🇳🇬Sanata Ibrahim Shekarau ya ba Gwamnatin Tarayya shawara kan kirkirar 'yan sandan jihohi a fadin Najeriya baki daya
Shekarau ya ce ya kamata a hana jami'an rike manyan makamai domin gudun dawo da 'yan daban siyasa a jihohi
Ya shawarci yin amfani da 'yan sandan a jihohi kamar yadda ya yi ga hukumar Hisbah a lokacin da ya ke mulki a Kano
🇳🇬Tsohon mataimakin gwamnan Edo ya tubure, ya ki dawo da motoci bayan an tsige shi a mulki.
Motocin da ake magana a kai su ne: Toyota Prado SUV 2, Toyota Hilux 1 sai Toyota Land Cruiser.
‘Dan siyasar ya ce mota 1 kurum ya samu a tsawon shekaru kusan 8 a mataimakin gwamna.
🇳🇬Aikin Raya Al'uumma Matattu samu sun Samu rabon su daga sanata Hanga, ya raba tallafin tukunya da likkafini miliyan 1 ga kakabartun shiyyar sa a Jihar Kano
🇳🇬Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin hana gayyatar da Babbar Kotun Jihar Kogi ta yi wa Shugaban EFCC, a ƙarar da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya maka EFCC, tun a farkon wannan shekara.
Manyan Alƙalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara bisa jagorancin Joseph Oyewole ne suka yanke hukuncin bada umarnin soke kiranyen da Kotun Kogi ta yi wa Shugaban EFCC, Olukoyede.
Lauyan Shugaban EFCC mai suna Jibrin Okutepa ne ya shigar da ƙarar, a madadin shugaban na EFCC
🇳🇬Yau shekaru 14 kenan da rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa 'Yar'Adua.
Tsohon shugaban ya rasu a ranar 5 ga watan Mayu, 2010 yana da shekaru 59.
Waɗan ne ayyukan alkhairai zaku iya tinanowa da yayi?
🇳🇬Aƙalla mutane 42 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ƙyanda a ƙananan hukumomin Mubi da Gombi a Jihar Adamawa.
Kwamishinan lafiya da ayyukan jin ƙai, Feliɗ Tangwame ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a ranar Juma’a.
🇳🇬Sabbin ma’aikatan jinya da ungozoma da aka ɗauka aiki a Jihar Kaduna sun yi kira ga Gwamna Uba Sani da ya sa baki a kan rashin biyan albashinsu na watanni takwas.
Sama da ma’aikatan lafiya 200 gwamnatin jihar ta ɗauka a watan Yunin 2023 a kan matakin albashi na 7 kuma aka tura su zuwa manyan asibitocin jihar
DAGA ƘASASHEN WAJE
🌍Jam'iyya da ke mulki a Togo ta samu gagarumar nasara a zaɓen majalisar dokoki da aka gudanar ranar 29 ga watan Afrilu, a cewar hukumar zaɓen ƙasar, bayan gyaran fuskar da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar wanda 'yan hamayya suka ce zai bai wa Shugaba Faure Gnassingbe ci gaba da mulki.
🌍Kasar Turkiyya ta dakatar da alaƙar kasuwanci da Isra'ila.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Turkiyya ta dauki matakin ne kan gallazawa Falasɗinawa da Isra'ila ke yi.
Kasar Isra'ila ta bayyana matakin da ta dauka kan lamarin.
FAGEN WASANNI
Real Madrid ɗin ta lallasa Cadiz da ci 3-0 da taimakon ƙwallayen da Brahim da Bellingham da kuma Joselu suka zura, amma nasarar lashe kanbin da sauran wasanni huɗu a hannu ta tabbata ne sakamakon dukar da Barcelona ta sha da ci 4 - 2 a fafatawar ta da Girona.
....................-----________
Allah ya gafarta mana mu da iyayen mu, Allah ya amshi ibadar mu, Allah biya mana buƙatun mu.
..........--------____........
MARUBUCI MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE
Comments
Post a Comment