Kamfanonin siminti sun ki amsa kiran majalisar wakilai.
ASSALAM ALAIKUM
YAU TALATA
13 GA ZUL QIDAH 1445
21 GA MAYU 2024
🇳🇬Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyyar mutuwar Shugaban Iran Ebrahim Raisi, da Ministan Harkokin Waje Hossein Amir-Abdollahian, da sauran abokan tafiyarsu sakamakon hatsarin jirgin sama.
Wata sanarwa daga fadar shugaban a Abuja ta ce Tinubu "ya bayyana damuwa game da wannan tsautsayi, kuma ya siffanta Raisi a matsayin shugaban da ya mayar da hankali wajen cigaban Iran.
🇳🇬Kungiyoyin kwadagon kasar nan sun bayyana cewa sun shirya halartar taron ci gaba da duba kan batun mafi karancin albashi a kasar nan a yau Talata ne kwamitin da gwamnatin tarayya ya kafa kan mafi karancin albashi zai sake zama da NLC da TUC bayan sun yi fatali da tayin farko Kwamitin dai ya yi tayin N48,000 lamarin da kungiyar ta yi fatali da shi, tare da bayyana cewa ba za ta amince da ko da tayin N100,000 ba.
Mataimakin shugaban kungiyar TUC ta manyan ma’aikatan kamfanoni da masana’antu, Mista Etim Okon, ya tabbatar da haka yau a Abuja.
🇳🇬Oba na Benin, Uku Akpolokpolo Ewuare II ya dira kan hukumar yaki da cin hanci ta EFCC inda ya ke zargin wasu jami'anta da karbar rashawa Sarkin ya nuna damuwa kan yadda wasu jami'an hukumar ke gudanar da ayyukansu ba tare da bin ka'ida ba yayin bincike Ya bayyana yadda ya so taimakon hukumar yayin binciken wasu daga fadarsa amma mai kula da binciken ta ba shi kunya.
Ya ba da misalin yadda aka cafke wasu masu mukami a fadarsa kan zargin damfara inda aka tasa keyarsu zuwa ofishin hukumar da ke birnin Benin. Mai sarautar ya ce wasu daga cikin jami'an sun share maganar zargin inda daga bisani suka sake su, "Muna son jan hankalinku kan wasu abubuwa da ba su kamata ba kan ayyukan da kuke yi." "Duk yadda ka yi kokarin taimakawa daga fada abin zai baka kunya, saboda na samu labarin cewa suna sauraron wasu ɓangarori kuma da wanda ya fi biya."
🇳🇬Kamfanonin siminti sun ki amsa kiran majalisar wakilai a jiya Litinin.
Majalisar ta gayyace su ne domin duba yiwuwar sauke farashi.
Shugaban kwamitin ya mika sako ga kamfanonin kan kaucewa kiran majalisar.
🇳🇬Rundunar ‘Yan Sandan Adamawa Ta Cafke Wata Mata Bisa Zargin Kona ’Ya’yanta Biyu
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wata mai suna Rachel Geoffrey, ‘yar shekara 23 da haihuwa, bisa zargin ta kona ’ya’yanta ‘yan shekara 7 da kuma dan shekara 3 da wuta mai tsanani.
A cewar rundunar ‘yan sandan, da gangan mahaifiyar ta kona hannun yaran a matsayin ladabtar da su kan cin abincin da ta ajiye wa mahaifinsu.
DAGA ƘASASHEN WAJE
🌍Shugaba Biden ya sake jaddada matsayar sa ta kare Isra’ila, sa’oi kaɗan bayan mai gabatar da ƙara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya ce ya nemi a bashi isinin kama Benjamin Netanyahu da kuma ministan tsaron sa, a bisa zargin aikata mummunan manyan lafuka a Gaza.
Da yake tsokaci a kan shari’ar da aka yi mataki-mataki a kotun ta duniya, Mr Biden ya haƙiƙance cewa dakarun Isra’ila ba su aikata kisan gilla a Gaza ba.
Da yake jawabi a fadar White House, lokacin wani tarom yahudawa, Mr Biden ya ce ko kusa babu-haɗi a tsakanin Isra’ila da Hamas.
🌍🌍Kafafen yada labarai a Iran sun ce za a gudanar da zaben shugaban kasa nan da ranar 28 ga watan Yunin gobe, bayan mutuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi.
Raisi ya rasu ne a ranar Lahadi sakamakon hadarin jirgin da ya rutsa da shi tare da Ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian.
Shugaban sojin kasar ya bayar da umarnin a gudanar da binciken dalilin hatsarin jirgin.
Gabanin zaben an ayyana mataimakin Raisi, Muhammad Mukhbir a matsayin wanda zai ci gaba da jagorantar kasar
FAGEN WASANNI
⚽Tsohon kyaftin din Super Eagles, Kanu Nwankwo, ya kai wa tsohon dan wasan Najeriya Tijjani Babangida ziyarar jaje bayan hatsarin mota da ya yi da iyalinsa, wanda ya yi sanadin mutuwar kaninsa da dansa.
..............-----------.......
Allah ya yaye mana dukkanin matsalolin day Suka addabe mu,ya gafarta mana,ya albarkaci Zuri ar mu,ya sanya alherin sa a gidajen mu.
...............----------
MARUBUCI
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE
Comments
Post a Comment