Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta ce ƙananan yara na zuwa kotu suna yin sabuwar takardar haihuwa domin su samu damar bude asusun banki da niyyar shiga harkokin damfara ta intanet (Yahoo boys).
ASSALAM ALAIKUM
YAU TALATA
06 GA ZUL QIDAH 1445
14 GA MAYU 2024
.
🇳🇬🇳🇬Shugaba Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da man fetur a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Najeriya.
Shugaban kasar ya kuma umarci motocin su koma amfani da ababen hawa masu amfani da iskar gas.
A jawabinsa ga Majalisar Zartaswa ta Kasa, Shugaba Tinubu, ya ce babu gudu babu ja da baya kan batun komawa amfani da ababen hawa masu amfani da iskar gas a Najeriya.
A cewarsa, hakan na daga cikin matakan da gwamnatinsa ta dauka na tabbatar da wadataccen makamashi da kuma rage tsadarsa a kasar.
🇳🇬Hukumar EFCC za ta sake gurfanar da Hadi Sirika da dan'uwansa a ranar Talatar nan, kan wasu laifuka 8 da ake zarginsu.
Dama dai a Alhamis din makon jiya aka gurfanar da Hadi Sirika da diyarsa Fatima da surukinsa a gaban kotu, daga bisani aka bayar da belinsu kan kudi Naira miliyan 100,kowanne su.
🇳🇬Gwamna Simi Fubara ya bayyana alamun zai bincike shekara 8 na tsohon uban gudansa kuma ministan Abuja, Nyesom Wike a Ribas Yayin rantsar da sabon Antoni Janar na jihar Rivers, Fubara ya ce zai kafa kwamitin da zai binciki yadda aka tafiyar da gwamnati kafin zuwansa Wannan na zuwa ne yayin da rikicin siyasar da ke tsakanin gwamnan da Wike ya dawo sabo a ƴan kwanakin.
🇳🇬Tsohon kakakin majalisar jihar Ribas, Edison Ehie, ya fallasa irin kullalliyar da aka kulla domin tsige Gwamna Siminalayi Fubara Mr Ehie ya tariyo yadda aka rika ba 'yan majalisar jihar makudan kudade domin su sa hannu a tsige gwamnan jihar na Rivers A yayin da ya ki karbar kudin, Mr Ehie ya ce an kulla masa makirci wanda ya ja har 'yan sanda suka fara nemansa ruwa a jallo
🇳🇬Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fara gudanar da cikakken bincike kan mumunan al’amuran da suka faru dangane da mutuwar jami’in kwastam da aka ce ya kashe kan shi ta hanyar harbin kansa da bindiga da kuma mutuwar wasu matasa biyu a rikicin baya-bayan nan da aka yi a unguwar Darmanawa da ke Kano.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya fitar ta hannun jami’in hulda da jama’a na runduna, SP Abdullahi Haruna Kiyawa.
Abubuwan da suka faru a lokuta daban-daban, sun haifar da damuwa a cikin al'umma inda aka dauki matakin gaggawa daga jami'an tsaro.
"Tun da farko dai, kisan kai na jami’in kwastam CSC Abdullahi Abdulwahab Magaji ya haifar da tambayoyi, lamarin da ya sa ‘yan sandan gudanar da bincike mai zurfi." in ji sanarwar
🇳🇬Shugaban Cocin Angalika Henry Nsukuba, ya yi wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kukan yadda ‘raɗaɗin tsadar rayuwa, fatara, talauci da yunwa ke ci gaba da nuƙurƙusar talakawan Najeriya’.
Ya shaida wa Tinubu cewa “maganar gaskiya da rayuwa ta yi wa ‘yan Najeriya masifaffiyar tsada a cikin ƙasar nan.”
Daga nan sai ya yi kira da a gaggauta bijiro da hanyoyin sauƙaƙa rayuwar al’ummar ƙasar nan.
🇳🇬 Dangin Namitra Bwala, dalibar kwalejin “Lead British International School” dake Gwarinpa, a birnin Abuja, sun maka makarantar a kotu.
Shigar da karar ya biyo bayan faifan bidiyon daya karade shafukan sada zumunta a ‘yan makonnin da suka gabata inda aka ga wasu dalibai suna cin zalin Namitra Bwala.
Haka kuma dangin dalibar na neman diyar Naira milyan 500, da neman gafara a jaridun Najeriya guda 2 saboda gazawar makarantar wajen sauke nauyin daya rataya a wuyanta na samawa ‘yarsu kyakkyawan yanayin neman ilimi.
Karar wacce aka shigar gaban Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja, tace gazawar makarantar wajen hana cin zalin dalibar, tare da gaggauta sanarda iyayenta da kuma gudanar da bincike akan lamarin har sai da bidiyon afkuwarsa ya karade shafukan sada zumunta alhalin tana karkashin kulawar makarantar, ya tabbatar da cewar akwai sakaci.
🇳🇬’Yan sanda a jihar Neja sun kama wata da ake zargin ’yar daba ce sanye da kayan sarki.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce jami’anta sun kama matar ne yayin wani rikicin daba a Anguwan-Kadara da ke yankin Maitumbi na jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Wasiu Abiodun ya ce, sun kama wadda ake zargin dauke da wuka a lokacin da suke fadan.
“A ranar 10 ga watan Mayun 2024 da dare, jami’anmu da ke sintiri a Maitumbi suka samu bayanan sirri dangane da wata ’yar daba da ke sanya kayan sarki.
🇳🇬Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta ce ƙananan yara na zuwa kotu suna yin sabuwar takardar haihuwa domin su samu damar bude asusun banki da niyyar shiga harkokin damfara ta intanet (Yahoo boys).
EFFC ta ce yaran suna kuma amfani da takarudn karin shekarun da suka samu wajen bude asusun banki da mallakar lasisin tuki daga hukumomin da abin ya rataya a wuyansu ne domin su ci moriyar abin da suka samu ta kazamar harkar zamba da yaudara.
Daraktan Hukumar EFCC na shiyyar Edo, Delta, da Ondo, Effa Okim, ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da kungiyar ’yan jarida ta kasa (NUJ) reshen jihar Edo ta kai masa
🇳🇬An bukaci Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya yi murabus daga kujerarsa.
Wani lauya daga jihar Taraba, Bilyaminu Maihanchi shi ya yi wannan kira.
Hakan ya biyo bayan matsanancin duhu da Arewa maso Gabas ke ciki kusan wata 1.
🇳🇬Wasu ƴan bindiga sun sace ma'aikatan kamfanin simintin Dangote a jihar Edo.
Maharan sun kai farmakin ne yayin da ma'aikata ke dawowa daga aiki a yankin Okpella kusa da Okene a jihar Kogi.
Yayin harin, miyagun sun kuma raunata wasu ma'aikatan da dama bayan bude musu wuta.
🇳🇬Gungun wasu barayi sun fatattaki masu gadin wasu manyan gonakin shinkafa, suka girbe ta suka yi awon gaba ita a jihar Taraba.
A cikin dare ne barayin suka shiga yankin Shimo da ake karamar hukumar Lau ta jihar, suka kori masu gadin suka girbe shinkafar suka tafi da ita.
Daya daga cikin masu gonakin, Abubakar Adamu, ya ce mai gadin da ya dauka aiki ya shaida masa cewa barayin sun zo ne da yawa dauke da muggan makamai. Abin da ya janyo dole suka ranta a ta kare domin tsira da rayukansu.
Ya ce, barayin sun iso gonakin ne da misalin karfe 12:30 na dare suka fara yankar shinkafar har zuwa asuba.
DAGA ƘASASHEN WAJE
🌍Majalisar Ɗinkin Duniya ta kaɗa ƙuri’ar amincewa ƙasar Falasɗinu zama cikakkar mamba a cikin majalisar.
Majalisar ta kuma yi kira ga Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince Falasɗinu ta zama ƙasa ta 194 a jerin mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya (UN).
A ranar Juma’a ce ƙasashe 194 suka jefa ƙuri’ar, wanda yunƙuri ne na amincewa da ƙasar Falasɗinu, bayan Amirka ya ƙi amincewa a watan da ya gabata.
🌍Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alƙawarin "korar" ɗaliban ƙasashen waje daga waɗanda suka shiga zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a jami'o'in Amurka daga ƙasar ta Amurka "nan take" idan aka sake zaɓensa a zaɓukan 2024.
DAGA FAGEN WASANNI
⚽Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta ƙaddamar da Finidi George a hukumance a matsayin kocin tawagar ƙasar ta Super Eagles na dindindin bayan sanar da sunansa a ƙarshen watan da ya gabata.
Tsohon ɗan wasan na tawagar Super Eagles, da ma shi ne ke jan ragamar tawagar na riƙon-ƙwarya tun bayan da ɗan ƙasar Portugal Jose Piseiro ya ajiye aikin bayan kammala gasar Kofin Afirka a Ivory Coast.
Da yake magana yayin gabatar da shi a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja, Ministan Wasanni John Enoh ya nemi NFF ta bai wa tsoohon ɗan wasan gefen dukkan taimakon da yake buƙata don ya yi nasara
⚽Yau Talata watakila ta kasance ranar bakin ciki ko farin ciki ga Tawagar Mikel Arteta....
Akwai tashin hayaki a kawunan yan Arsenal, Ko Tottenham ta taimaka musu ta doke Manchester City domin a ranqr karshe su samu karfin lashe Premier League ko kuma taki tausaya wahalarsu.
00p00p0pp
⚽Kylian MbAppé ya lashe kyautar mafi kyawun dan wasan a Ligue 1.
“Ina godiya ga daukacin mutanen kungiyar PSG, da kuma shugaban kulab din. Zan rasa su. Zan tafi tare da rike kaina," in ji Mbappé.
⚽Bayan ya zura ƙwallo ta biyu ga Barcelona a wasan da suka buga da Real Socieded, Raphinha ya cire rigar sa domin nuna ƴar ƙaramar rigar sa ta cike wadda ke ɗauke da rubutun ‘Ku yiwa RS Addu'a’, Bayan iftila'in ambaliyar ruwa da ya faɗawa Jihar Rio Gran de Soul ta ƙasar Brazil a makon da ya gabata.
..,................----------___
Allah ya haɗa mu da alherin wannan rana ta Talata.Allah ya gafarta mana mu da iyayen mu.
-------------.........-------
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE
Comments
Post a Comment