Nan da watan Yuni Najeriya za ta kawo karshen shigo da man fetur.
ASSALAM ALAIKUM
YAU LAHADI
11 GA ZUL QIDAH 1445
19 GA MAYU 2024
🇳🇬Kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa kan sabon mafi ƙarancin albashi a ƙasar zai sake zama a mako mai zuwa domin ci gaba da tattauna batun mafi ƙarancin albashin ma'aikatan ƙasar, bayan da ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar suka fice daga tattaunawar ranar Larabar da ta gabata 15 ga watan Mayu.
Cikin wasiƙar gayyatar da shugaban kwamitin, Bukar Goni, ya aike wa mambobin kwamitin a matakan jihohi ya ce kwamitin ya amince da sauya matsayarsa kan naira 48,000 da ya ɗauka ranar Larabar.
Wasiƙar ta yi kira ga shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar, da su gayyaci mambobinsu domin halartar zaman da za a yi ranar Talata 21 ga watan Mayu.
🇳🇬Ƙungiyar gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda suka ce gwamnatin tarayyar na nuna musu wariya a ɓangren ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke yi, musamman titunan mota da layin dogo da za su haɗa yankin da sauran sassan ƙasar.
Gwamnonin - da suka haɗa na jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba da kuma Yobe - sun gudanar da taron ƙungiyar ne karo na 10 ranar Juma'a a jihar Bauchi.
Cikin sanarwar bayan taro da gwamnonin suka fitar, sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta dubi yankinsu wajen samar da waɗannan abubuwan more rayuwa
🇳🇬Hukumar Alhazan Najeriya, Nahcon na ci gaba da jigilar maniyyatan ƙasar zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce zuwa yau Asabar da safe jirage 12 ne ɗauke da maniyyatan ƙasar 5074 suka isa Saudiyya.
Hukumar ta ce 11 daga cikin jiragen sun sauka ne a birnin Madina, yayin da ɗaya kuma ya sauka a Jedda.
Nahcon ta ce daga cikin adadin maniyyatan ta suka isa ƙasa mai tsarkin 2934 maza ne, yayin da 2140 kuma mata ne.
🇳🇬Nan da watan Yuni Najeriya za ta kawo karshen shigo da man fetur - In ji Ɗangote
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, kuma shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote, ya ce biyo bayan tsare-tsare na matatar man dangote, Najeriya ba za ta kara neman shigo da mai daga wata mai zuwa.
Dangote ya kuma bayyana cewa matatar sa za ta iya biyan bukatun man fetur da dizal a yammacin Afirka, da kuma biyan bukatar man jiragen nahiyar Afrika.
🇳🇬Kwamitin malaman addinin musulunci na Najeriya ya goyi bayan auren marayu 100 da kakakin majalisar dokokin jihar Neja ya ƙuduri aniyar ɗaukar nauyi.
Cikin wata takarda da kwamitin ya fitar, mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin, Malam Aminu Inuwa Muhammad da sakatarensa, Engr Basheer Adamu Aliyu, sun ce abin da kakakin majalisar ke shirin yi abin a yaba ne, ba na kushewa ba.
Kwamitin ya ce duba da matsalar tsaro da matsin tattalin arziki da wasu yankunan arewacin Najeriya ke fuskanta, ɗaukar nauyin aure wani nau'i ne na tallafa wa marasa ƙarfi
🇳🇬Shugaban jam'iyyar SDP na Najeriya, Shehu Gabam ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da ta gabata da rashin magance matsalolin Najeriya, lamarin da ya ce ya haifar wa gwamnati mai ci fusknatar tarin matsalolin tattalin arziki.
Yayin wata hira a shirin 'Politics Today' na gidan Talbijin na Channels, Gabam ya zargi gwamnatin Buhari da gazawa wajen magance matsalolin ƙasar
DAGA ƘASASHEN WAJE
🌍Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ka iya ƙara zafafa hare-harenta a arewa maso gabashin Ukraine bayan galabar da ta samu a baya-bayan nan a kusa a birnin Kharkiv.
Dakarun Rasha nba yunƙurin dannawa a yayin da sojojin Ukriane ke fuskantar koma baya sakamakon rashin makamai.
Mista Zelensky ya amince cewa sojojinsa na fuskantar ƙarancin makami da ƙwarin gwiwa, yana mai cewa babu sojoji a mafi yawan sansanonin sojin yankin
🌍Wata kotu a Amurka ta yanke wa wanda ya kai wa mijin tsohuwar kakakin majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosy, hukuncin ɗaurin shekara 30 a gidan yari.
Kotun ta samuDavid DePape da laifin kai wa Paul Pelosi hari tare da yunƙurin garkuwa da shi a watan Nuwamban bara.
A lokacin harin David DePape ya fasa wa Paul Pelosi mai shekara 84 kai, lamarin da ya sa ya kwashe kusan kwana shida asibiti likitoci na ba shi kulawa
🌍Ministan yakin Israila Benny Gantz ya yi barazanar yin murabus daga majalisar yakin kasar idan Benjamin Netanyahu ya ki bayyana shirinsa na kula da Gaza bayan yakin yazo karshe.
FAGEN WASANNI
⚽Yau Lahadi ita ce za ta kasance ranar karshe da za a rufe wasu daga cikin gasannin nahiyar Turai da wasu sassan duniya.
Tuni a wasu gasannin aka samu wadanda suka lashe su, kamar Bundesliga da La Liga da Serie A.
Sai dai har yanzu Firimiyar Ingila akwai sauran rina a kaba, domin kuwa wasan da ya rage shi ne zai bayyana gwarzon gasar tsakanin kociyan Manchester City, Pep Guardiola da takwaransa na Arsenal, Mikel Arteta.
A yanzu haka teburin gasar ya nuna Manchester City ce ke jagorantar Firimiyar da maki 88 tazarar maki biyu tsakaninta da Arsenal.
Ita kuwa Arsenal da ke mataki na biyu da maki 86, ta zarce Manchester City da kwallo guda, inda take da 61 ita kuma City na da 60.
A wasan na ranar Lahadi, Manchester City ta kece raini da West Ham, yayin da Arsenal za ta barje gumi da Everton.
🌍Pep Guardiola ya tabbatar da shirinsa na ci gaba da zama kocin Man City a kakar wasa mai zuwa.
"Ina da kwantiragi kuma ina so na kasance a nan Man City kakar wasa mai zuwa, ba shakka! Zan zauna a nan City."
Guardiola zai ci gaba da zama a Man City har zuwa watan Yuni 2025 ba tare da la'akari da abin da zai faru a wasanni biyu masu zuwa ba na kungiyar ba.
.........................
Allah ya gafarta mana zunuban mu ya haɗa mu da alherin wannan rana ta Lahadi.
.....,......................
MARUBUCI MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE
Comments
Post a Comment