Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya rasu sakamakon hatsarin jirgin helikwafta
AS-SALAM ALAIKUM
YAU LITININ
12 GA ZUL QIDAH 1445
20 GA MAYU 2024
🇳🇬Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ajuri Ngelale matsayin wakilin shugaban kasa na musamman kan ayyukan sauyin yanayi Haka zalika, Ngelale ne sakataren sabon kwamitin mutane 25 da aka kafa kan shirin tattalin arziki na Green Economic Initiatives (GEI) Kafin wannan nadin, Ajuri Ngelale shi ne mai ba Tinubu shawara na musamman kan harkokin yada labarai.
🇳🇬Ɗan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a Zaɓen 2023, Peter Obi, ya ziyarci waɗanda harin masallaci ya rutsa da su a Jihar Kano.
Peter Obi wanda a jiya Lahadi ya sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, kai tsaye ya wuce Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, inda wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa ke jinya.
A jawabinsa, Peter Obi ya ce, “wannan abu ne mai ban tsoro da dole a yi Alla wadai da shi.
“Abin baƙin ciki ne irin wannan lamari na iya faruwa a ƙasarmu a yau.
“Ba wanda zai iya faɗin wani dalili da zai sanya wannan matashi ya kai wa ’yan uwansa irin mummunan hari.
“Duk da haka ba za mu daina yin Allah wadai da irin wannan aika-aikar a kan mutane ba.
“Dalilin wannan ziyara da na kawo shi ne jajanta wa waɗanda lamarin ya shafa da nuna damuwa kan irin raɗaɗin da suke ɗanɗanawa
🇳🇬An shiga jimami bayan babbar mota ta murkushe bas guda 4 a jihar Imo.
Akalla mutane 15 ne aka ruwaito sun mutu a hadarin, inda aka tattara wasu zuwa asibiti.
Hadurran mota sun zama ruwan dare a Najeriya, ana yawan asarar rayuka.
Shaidun gani da ido sun shaidawa jaridar Premium Times, cewa da alama motar ta samu matsala a birki ne wanda ya kai ga aukuwar hadarin.
DAGA ƘASASHEN WAJE
Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya mutu sakamakon hatsarin jirgin helikwafta
Kamar yadda wani jami'in gwamnatin ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ce shugaban kasar ya rasu ne tare da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian
🌍Burkina Faso da Mali da Nijar da ke ƙarƙashin mulkin soja, sun kammala shirye-shiryen samar da ƙungiyar gamayyar ƙasashen.
Lamarin na zuwa ne bayan da ƙasashen suka juya wa Faransa da ta yi musu mulkin mallaka baya, inda suka karkata akalarsu wajen Rasha a yanzu.
🌍Rundunar Sojin Jamhuriyar Dimokuraɗiyya Kongo ta ce ta daƙile juyin mulkin da wasu ’yan ƙasar da na ƙetare suka yi yunƙurin yi wa Shugaba Felix Tshikedi a Kinshasa, babban birnin ƙasar.
Rundunar ta ce an yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar ne da sanyin safiyar ranar Lahadi a kofar gidan Ministan Kula da Tattalin Arziki da ke yankin Gombe, inda nan ne ofishoshin shugaban kasar yake.
Cikin wani jawabi da ya fitar ta gidan talbijin na ƙasar, mai magana da yawun sojojin ƙasar, Burgediya Janar Sylavin Ekenge, ya ce a yanzu ƙura ta lafa, kuma sojojin ƙasar na tsare da wasu da ake zargi da hannu a lamarin.
FAGEN WASANNI
⚽An ɓarke da shewa a filin wasa na Etihad bayan da Man City ta doke West Ham da ci 3-1, yayin da Arsenal kuma ta yi nasara a kan Everton da ci 2-1 a Emirates.
Hakan na nufin City ta ƙare da maki 91, Arsenal kuma na da 89.
⚽Dandazon magoya bayan kungiyar Manchester City sun yi dafifi a cikin filin wasa na Etihad inda suke murnar lashe gasar firimiyar bana.
🏐Arsenal a gasar Premier League ta bana:
• Babu wata ƙungiya a cikin manyan ƙungiyoyi shida na gasar da suka samu nasara akan su
• Ƙungiya ta biyu mafi yawan zura ƙwallaye
• Ƙungiya mafi ƙarancin zura mata ƙwallaye
• Ƙungiya mafi ƙarancin kaiwa
Akwai taɓa zuciya bayan wannan namijin ƙoƙarin batare da ka lashe kofin ba! 💔
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,........
Allah ya gafarta mana mu da iyayen mu Allah ya sanya tausayin mu a zukatan shugabanin mu.Allah ya haɗa mu da alherin wannan rana ta Litinin.
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
MARUBUCI MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE
Comments
Post a Comment