Shugaban kamfanin Binance ya yi zargin an nemi na goro a hannun jami'ansa.



ASSALAM ALAIKUM 

YAU LARABA 

29 GA SHAWWAL 1445

8 GA MAYU 2024

🇳🇬Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana cewa shugaba Tinubu da mukarrabansa za su dawo Najeriya daga Turai a yau Laraba

Mashawarci na musamman kan bayanai da dabaru ga shugaban kasar Bayo Onanuga ne ya sanar a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X yau Talata.

Indai za'a iya tunawa a ranar 22 ga Afrilu, Shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa kasar Netherlands a wata ziyarar aiki da yakai.

🇳🇬Babban bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da karɓar la'ada daga masu yin ajiya a bankuna.

CBN ya ba da wannan sabon umurnin ne ga bankunan kasuwanci.

Sai dai, dakatarwar na ɗan wani lokaci ne domin za a dawo a ci gaba da karɓa a nan gaba.
🇳🇬CBN ya umurci masu sana’ar POS da su yi rajista da gwamnati 

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa’adin wata biyu ga masu amfani da PoS da su kammala yin rajista da hukumar CAC mai yi wa kamfanoni rajista.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban hukumar ta CAC, Hussaini Magaji SAN ranar Talata a Abuja.

A cewar Magaji, wa’adin watanni biyun wanda zai kare a ranar 7 ga watan Yuli ya yi daidai da ka’idojin doka da kuma umarnin babban bankin kasa.
🇳🇬Jami'an EFCC sun titsiye wasu manyan jami'an rundunar tsaro NSCDC kan wawure kuɗi N6bn

🇳🇬  Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya ce yana iasasshen man da zai wadaci 'yan kasar na tsawon kwanaki 30 ba tare da wata tangarda ba.

Kamfanin a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X da DCL Hausa ta bibiya, ya shawarci 'yan kasar cewa babu bukatar su rika turoroniya wajen sayen man a halin da ake ciki

🇳🇬Jam'iyyar APC ta buƙaci majalisar dokokin jihar Ribas ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan mulki nan take APC ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan kalaman da Fubara ya yi kan sulhun da Bola Tinubu ya masu a rikicin siyasar Ribas Gwamnan dai ya ce sulhun da aka yi ba ya cikin kundin tsarin mulki, inda ya ƙara da cewa doka ba ta san da zaman majalisar dokokin ba Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar 


🇳🇬Shugaban kamfanin Binance ya yi zargin an nemi na goro a hannun jami'ansa.

Richard Teng ya yi zargin cewa wasu mutane sun buƙaci a ba su cin hanci domin kawar da zarge-zargen da ake yi kamfanin na kirifto.

Gwamnatin Najeriya dai na tuhumar jami'an na Binance da ƙin biyan kuɗaɗen haraji da sauran laifuffuka.

🇳🇬An bai wa kamfanonin simintin Dangote Cement da BUA da IBETO da sauransu wa’adin kwanaki 14 su gurfana a gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Wakilai domin amsa tambayoyi game da tsadar siminti a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan gazawar da kamfanonin suka yi wajen halartar zaman binciken da kwamitin yi gudanar ranar Talata.

Kwamitin haɗin gwiwar wanda ya ƙunshi kwamitocin majalisar mai kula da ma’adanai da kasuwanci da masana’antu da ayyuka na musamman, majalisar ta kafa shi ne domin binciken ƙarin farashin siminti a Najeriya ba da kamfanonin suka yi.

Majalisar ta kuma gayyaci Ministan Ma’adanai, Dele Alake, da ya gurfana gaban kwamitin ranar Talata 19 ga Mayu, 2024, bayan ya kasa bayyana a Talatar nan.


🇳🇬Darakta-Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana cewa hukumar ta aikawa Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) sama da Naira biliyan 18 domin shirye-shiryen aikin hajjin shekarar 2024.

Sanarwar da kakakin hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar ta ce, duk da cewa mutane 3,110 sun biya kuɗin aikin hajjinsu, yawancinsu suna jiran bizarsu daga Hukumar NAHCON.

DAGA ƘASASHEN WAJE 

🌍Dakarun sojin Jamhuriyar Nijar sun kama wani jagoran ’yan bindigar Najeriya, Kachallah Mai Daji a kusa da iyakar garin Illela da ke kasar.

Masanin harkar tsaro kuma mai sharihi kan yaki da tayar da kayar baya a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce sojojin Nijar sun kama dan bindigar ne a lokacin da yake kokarin sace dabbobi ya tsallaka iyakar Najeriya da Nijar da su.

🌍Hamas ta ce ƙudirin firaiministan isra'ila, Benjamin Netanyahu na shiga Rafah ya nuna cewa da shi da sojojin Isra'ila suna son waɗanda ake garkuwar da su su mutu.



FAGEN WASANNI 
⚽Manchester United za ta raba gari da kocinta Erik ten Hag da zaran an kammala wasan karshe na FA a ranar 25 ga watan Mayu.

⚽Dortmund ta yi wa PSG gida da waje a Gasar Zakarun Turai, jimilla PSG 0-2 Dortmund.
⚽Mbappe ya fice daga ɗakin taron manema labarai batare da ya bada amsa ba bayan wani ɗan jarida ya masa tambaya akan shin ko zai goyawa Real Madrid baya a wasan da zasu buga da Bayern Munich.
⚽A Hukumance: Cole Palmer ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Chelsea na kakar wasan 2023/24 ɓangaren maza.


Ɗan wasan yabi sahun ƴan wasa irin su Eden Hazard, Thiago Silva da Willian a matsayin ƴan wasan Chelsea da suka lashe kyautar gwarzon ɗan wasan ƴan wasa da kuma Gwarzon ɗan wasan Chelsea a kakar wasa guda.


__.…................  .       

Allah ya  haɗa  mu da alherin  wannan rana ta Laraba Allah ya amshi ibadar mu Allah ya gafarta mana mu da iyayen mu.


..................
MARUBUCI
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE

Comments

Popular posts from this blog

Kotun kolin kasar nan ta sanya yau Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar

Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal