Wasu gwamnonin jihohin Najeriya sun ƙara albashin ma'aikatan gwamnati a jihohinsu saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar nan.



ASSALAM ALAIKUM 

YAU ASABAR 

25 GA SHAWWAL 1445

4 GA MAYU 2024


,
🇳🇬Tsohon hafsan sojojin ruwa a Najeriya, Usman Jibrin ya shiga matsala bayan umarnin wata babbar kotu a Abuja Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin cafke Jibrin da wasu mutane uku kan badakalar makudan kudi har N1.5bn Lauyan hukumar yaki da cin hanci, Osuobeni Ekoi Akponimisingha shi ya shigar da korafi kan mutanen ukun.

🇳🇬 Har yanzu dai Najeriya na fama da hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce akwai laifin gwamnati da 'yan majalisu a tashin kayan.

Cardoso, ya ce sayen kayan abinci mai yawa da aka yi domin rabawa talakawa ya jawo tsadar kayyayaki.



🇳🇬Gwamna Alex Otti ya kafa kwamitin tsaro a jihar Abia.

Gwamna ya naɗa tsohon shugaban sojojin Najeriya, Laftanar-janar Azubuike Ihejirika.

Ihejirika zai jagoranci kwamitin tsaron jihar da sauran kwararru a harkar tsaro.

🇳🇬Wasu gwamnonin jihohin Najeriya sun ƙara albashin ma'aikatan gwamnati a jihohinsu saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar nan. 
Ma’aikatan gwamnati a faɗin ƙasar nan sun yi ta kokawa domin samun ƙarin albashi saboda halin da tattalin ƙasar nan ya tsinci kansa a ciki. 
Wasu daga cikin ma'aikatan kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu inda aka yi musu ƙarin albashi. 
Ga jerin sunayen gwamnonin jihohin Najeriya da suka amsa kiran ma’aikata tare da ƙara musu albashi. 
Na farko a jerin sunayen shine Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo. Obaseki ya sanar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan jihar a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu. 
Na biyu Gwamna Bassey Otu ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N40,000 ga ma’aikatan gwamnati a jihar Kuros Ribas. Gwamnan na jam’iyyar APC ya ce sabon tsarin albashin ya yi dai-dai da abin da jihar za ta iya biya, duba da yanayin kason da take samu daga gwamnatin tarayya 
Wani gwamnan APC da ya yi wa ma’aikatan gwamnati ƙarin albashi a jiharsa shi ne Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi. 
Wannan ci gaban ya zo ne watanni takwas bayan gwamnan ya ƙara Naira 10,000 ga albashin ma’aikatan jihar Ebonyi.
🇳🇬Gwamnan Zamfara ya dakatar da shugaban hukumar ZAROTA da gaggawa 

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya amince da dakatar da shugaban hukumar kula ababen hawa ta jihar ZAROTA Abubakar Mailambu daga mukaminsa.

A cikin wata sanarwa daga Sakataren Gwamnatin jihar Malam Abubakar Nakwada, ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take.
🇳🇬Wasu mutane da suka bayyana kan su a matsayin 'yayan jam'iyyar APC daga Jihar Zamfara dake Najeriya sun yi tattaki zuwa ofishin hukumar EFCC dake Abuja, inda suke bukatar ganin an sake kakkabe kurar dake takardun zargin da ake yiwa tsohon gwamnan jihar kuma ministan tsaro Bello Matawalle na karkata kudaden da suka kai naira biliyan 70 lokacin mulkinsa

DAGA FAGEN WASANNI 
⚽Tsohon kocin Chelsea da ke horar da Bayern Munich Thomas Tuchel na cikin jeren mutanen da za su iya maye gurbin Erik ten Hag idan ya bar Manchester United a wannan kaka.

⚽Foden ya doke Declan Rice na Arsenal da kuma Rodri na Man City don samun kyautar ta ƙungiyar marubutan wasanni ta Ingila.
---------_____----------------
Allah ya gafarta mana mu da iyayen mu, Allah ya sanya tausayin mu a zukatan shugabanin mu, Allah ya karɓi ibadun mu.
_----+++------------_---__----__--_---
MARUBUCI
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE.

Comments

Popular posts from this blog

Kotun kolin kasar nan ta sanya yau Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar

Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal