‘Yan Najeriya sama da miliyan daya ne suka mika takardar neman sabon tsarin basussuka









ASSALAM ALAIKUM 

YAU LARABA

07 GA ZUL QIDAH 1445

15 GA MAYU 2024

🇳🇬Majalisar ministocin Najeriya ta amince da kashi na 2 na kwangilar aikin gina hanya tsakanin Lagos zuwa Calabar wadda zata lashe naira triliyan guda da biliyan dubu 600 da kuma hanya tsakanin Sokoto zuwa Ilela da Badagry domin hadewa da ta Lagos.
🇳🇬Shugaban hukumar aAlhazan Najeriya, Jalal Arabi tare da tawagar hukumar jin ɗaɗin Alhazai ta kasa sun sauka Kebbi ranar Talata.

Shugaban na NAHCON tare da maƙarrabansa da wasu jigajigan gwamnati za su ƙaddamar da fara jigilar maniyyata zuwa Ƙasa mai tsarki daga gobe Laraba.

Shugaban hukumar jin dadin alhazai na jihar Kebbi Faruku Yaro ne ya tarbi tawagar Arabi a filin jirgin sama na Kebbi.

Ana sa ran shugaban Kasa, Bola Tinubu, Matamakinsa Kashim Shettima za su halarci taron ƙaddamarwar.

Akalla maniyyata 64,000 ake sa ran za su yi aikin Hajji bana daga kasa Najeriya

🇳🇬KNSG ARTV MD, Daya Daya Kotu Akan Zargin Kudade

 Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Manajan Daraktan Gidan Talabijin na Abubakar Rimi, Mustapha Adamu Indabawa da Jami’in Ma’aikata, Ibrahim M. Bello, da laifuka guda bakwai, da suka hada da hada baki, karkatar da kudade da kuma karkatar da kudade da dai sauransu.

 Bukatar fifita tuhumar mutanen biyu a karkashin sashe na 211 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya 1999 (Kamar yadda aka gyara) da sashe na 121 (1), 123 (1) (a) 126 (b) da 377 na Gwamnatin Jihar Kano.  na dokar shari’a ta manyan laifuka (2019) da ‘The Historica Nigeria’ ta gani a ranar Talata, mai kwanan wata 14 ga Mayu, 2024, an makala da takardar tuhumar, da jerin shaidu da bayanansu, da takaitaccen bayani na shaidu, da takaitattun shaidu da  kwafin maganganun waɗanda ake tuhuma da sauran abubuwan baje koli.

 Hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ce ta shigar da karar a karkashin dokar da babban lauyan jihar ya yi mata.

 Rahoton ya ce hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta jihar ta binciki lamarin biyo bayan wata koke da aka rubutawa gwamnan jihar kan shugaban hukumar ta ARTV, Mustapha Adamu Indabawa.

 Kamar yadda majiya mai tushe ta tabbatar da cewa hukumar yaki da sana’o’in hannu bayan da ta gudanar da bincike ta gano dimbin ayyukan ta’addanci a gidan talabijin din da ya sa aka kai mutanen biyu kotu bayan mika rahoton ga Gwamnan.


🇳🇬‘Yan Najeriya sama da miliyan daya ne suka mika takardar neman sabon tsarin basussuka, inji gwamnatin tarayya a ranar Talata.

 Wannan bayanin ya fito ne daga wurin Babban Manaja kuma Babban Jami’in Zastaswa Na Hukumar Kula da Kare Kayayyakin Kasuwa wato CREDICORP wanda ya ce adadin ‘yan Najeriya miliyan 1.6 ne suka mika takardun neman bashi.

A ranar 21 ga Afrilu, shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da kashi na farko na tsarin ba da lamuni na Consumer Credit Scheme. Shirin da zai bai wa 'yan ƙasa masu aiki damar samun lamuni don sayayyar kayayyaki masu mahimmanci. Makwanni uku bayan fara shirin, shugaban na CREDICORP ya bayyana cewa yawan takardun masu nema da aka samu zuwa yanzu na da yawa.


🇳🇬🇳🇬Za mu durkusar da al'amura idan har ba a kara wa ma'aikata albashi ba - NLC ta bai wa Shugaba Tinubu gargadi 

Kungiyoyin kwadagon sun kuma tsaya tsayin daka kan kudirinsu na biyan mafi karancin albashi na N615,000 yayin da suka dage a ranar 31 ga Mayu, 2024.

Wannan ci gaban ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya na gabatar da mafi karancin albashin ma’aikata ga ‘yan Najeriya biyo bayan karewar tsohon mafi karancin albashi a ranar 18 ga Afrilu, 2024.


🇳🇬 Kungiyar malaman jami’o’in Nijeriya, ASUU, ta yi barazanar tsunduma yajin aiki a yayin da take kokawa kan gazawar gwamnatin tarayya ta nada majalissar gudanarwar jami’o’in tarayya.

🇳🇬 Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta umurci dukkan masallatanta na Kamsus Salawatna Jihar Gombe da su fara gabatar da Alkunut saboda neman sauki daga tsada da kuncin rayuwa da ake fama da ita.

Shugaban kungiyar Jama’atu a Jihar Gombe, Injiniya Salisu Muhammad Gombe ne ya bada sanarwar hakan.





🇳🇬Jami’an tsaro sun kama wani ‘dan kunar bankin wake’ da ya yi barazar tayar da bom din da ke jikinsa a cikin banki a Jos, fadar Jihar Filato.

A safiyar Litinin ne matashin da ke daure da ababen fashewa a jikinsa ya shiga reshen Bankin UBA da ke unguwar Dadinkowa a garin Jos, ya nemi a ba shi kudi Naira miliyan 100, ko ya tayar da bom din.

Wani jami’in bankin da ya nemi a boye sunansa ya ce ma’aikatan bankin suna tsaka da kula da kwastomomi ne matashin ya yi barazanar tayar da bom din.

A cewarsa, dan kunar bakin waken ya yi basaja ne kamar kudi zai cira, ya je kan kanta ya shaida wa jami’in bankin cewa akwai bom a jikinsa kuma idan ba a yi abin da yake so ba zai tayar da bom din.

FAGEN WASANNI 
⚽Kungiyar Manchester City ta yi nasarar doke Tottenham Hotspur da ci 2-0 a wasan firimiyar kasar Ingila mako na 37.

Ko kuna ganin wannan nasara da Cityn suka yi na iya zama barazana ga kungiyar Arsenal a kokarin da take na lashe kofin a bana?
⚽Bayern Munich na zawarcin ɗan wasan tsakiyar Manchester United Bruno Fernandes a wannan kaka, kuma suna da yaƙinin cimma yarjejeniya da ɗan wasan na Portugal mai shekara 29. (Independent)

Manyan 'yan wasan Bayern Munich ciki harda ɗan kasar Ingila Harry Kane, mai shekara 30, na son kocinsu Thomas Tuchel ya sauya ra'ayi kan yunkurin barin kungiyar ta Bundesliga a karshen kaka. (Abendzeitung - in German)

Manchester United na son gabatar da tayin fam miliyan 55 kan ɗan wasan Everton da Ingila, Jarrad Branthwaite, mai shekara 21
⚽A Hukumance: Aston Villa zata buga gasar zakarun nahiyar Turai a kakar wasa mai zuwa!

Wannan shine karo na farko da ƙungiyar zata fafata gasar tun shekarar 1982 zuwa 1983.



..,................----------___
Allah ya haɗa mu da alherin wannan rana ta Talata.Allah ya gafarta mana mu da iyayen mu.
-------------.........-------
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE

Comments

Popular posts from this blog

Kotun kolin kasar nan ta sanya yau Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar

Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal