Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilinta na kin tayin abin da ya wuce ₦60,000 ga ma'aikata.
ASSALAM ALAIKUM
YAU LAHADI
25 GA ZUL QIDAH 1445
2 GA YUNI 2024
🇳🇬Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su zakulo wadanda suka kashe sojojin kasar a Aba tare da masu bada umarnin cewar mutane su zauna cikin gidajen su. Tinubu yace wannan abinda suka aikata cin amanar kasa ne, saboda haka ya bada umarnin yin dirar mikiya a kan duk masu kai irin wannan harin kan jami'an tsaron dake aikin kare lafiyar jama'a.
🇳🇬Bello Matawalle ya yi Allah wadai da kisan aka yiwa sojoji a jihar Abia.
Ƙaramin ministan tsaron ya sha alwashin cafko masu hannu a lamarin.
An dai hallaka sojojin ne yayin da suke a bakin aiki.
🇳🇬Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilinta na kin tayin abin da ya wuce ₦60,000 ga ma'aikata.
Kungiyoyin kwadago a kasar na neman gwamnati ta biya ₦494,000 a matsayin albashi ma'aikata.
Amma wasu dalilai 14 gwamnatin ta lissafa da cewa su ne suka hana ta wani tayi mai gwabi.
🇳🇬Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya koka kan halin da kasa ke ciki kafin barin mulki a 2015.
Jonathan kafin barin mulki ya tausayawa gwamnatin da za karbi ragamar kasar a wancan lokaci.
Ya ce tabbas gwamnatin za ta fuskanci kalubale da matsaloli da dama.
🇳🇬Gwamna Buni ya cika alƙawari, ya baiwa mahajjatan jihar Yobe tallafin N179.8m.
Hukumar alhazai ta ce an gama jigilar maniyyatan zuwa birnin Madinah.
Gwamma Buni ya yaba da yanayin aikin jigilar ya buƙaci alhazan su sa Najeriya a addu'a.
🇳🇬Ranar Litinin da za a fara yajin aiki ce ranar fara jarrabawar WAEC.
Hukumar ta bukaci daliban su fito domin rubuta jarrabawarsu.
Jami'ar WAEC a Ekiti T.A.Y Lawson ta ce ba a kasar nan kadai ake WAEC ba a ranar.
🇳🇬Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wani mutum da ake zargi da yunƙurin sayar da ’yar cikinsa mai shekara biyar a duniya kan kuɗin Naira miliyan 1.5.
Wanda ake zargin mai suna Yusuf Umar mai shekara 49, ya bayyana cewar yana aiki da ƙaramar hukumar Warji ne.
A cewar rahoton ’yan sandan, Umar, ya riga ya shirya miƙa yarinyar ga wani mutum, sai dai ya yi rashin sa’a wanda zaj sayi yarinyar jami’in ɗan sanda ne da ke aiki a sirri.
“A ranar 26 ga watan Mayu, 2024, wanda ake tuhuma ya ɗauki yarinyar ’yar shekara biyar daga wajen mahaifiyarta a ƙaramar hukumar Warji kan cewar zai kai ta wajen ’yar uwarsa da ke garin Bauchi.
“Mahaifiyar ba ta da masaniyar cewar ya shirya miƙa yarinyar ga waniutum, ba tare da sanin cewa shi jami’in ’yan sanda ne ba,” in ji Kwamishinan ’yan sandan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne a wani otal da ke Bauchi.
DAGA ƘASASHEN WAJE
🌍Sa'o'i 24 bayan kotu ta samu tsohon shugaban Amurka Donald Trump da laifuffuka 34, magoya bayan sa sun tara masa dala miliyan 54 domin ci gaba da yakin neman zaben da yake yi.
FAGEN WASANNI
⚽Zakarun Sifaniya Real Madrid sun yi wa Dortmund kwaf ɗaya cikin minti goma a Wembley.
Dani Carvajal da Vinicius ne suka jefa ƙwallayen, bayan da Dortmund ta zubar da damarmaki a zangon farko na wasan.
⚽Tsohon kyaftin din Manchester City Vincent Kompany ya maye gurbin Thomas Tuchel a matsayin sabon kocin Bayern Munich kuma shi ne bakar fata na farko da ya zama kocin kungiyar. Mun yi nazari kan abin da ya sa ba sa samun bakaken fata da suka zama koci a manyan kungiyoyin nahiyar Turai.
-_-------------------_----------_----_
Allah ya haɗa mu da alherin wannan rana ta Talata.Allah ya gafarta mana mu da iyayen mu.
-------------.........-------
MUHAMMAD AUWAL SULEIMAN DUTSE
Comments
Post a Comment